Ministan kula da harkokin wajen kasar Ghana Samuel Okudzeto Ablakwa ya ce, kasarsa da Sin na fadada dangantakarsu ta hanyar karfafa harkokin diplomasiyya da zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da shirye-shiryen hadin gwiwa na neman ci gaba.
Ministan ya bayyana haka ne lokacin da yake bayani game da ayyukan ma’aikatarsa cikin watanni 8 da suka gabata, karkashin wani shirin gwamnatin kasar na tsare gaskiya, inda ya ce Ghana na daya daga cikin kasashen Afrika na farko-farko da suka ci gajiyar manufar soke haraji ga kayayyakin da ake fitarwa daga kasashen zuwa kasar Sin.
Ya ce, sun fara tattaunawa da kasar Sin kan shirye-shirye da dama, ciki har da kafa cibiyar harhada ababen hawa masu amfani da lantarki da samar da sanholo daga ruwan bauxite da fara zirga-zirga kai tsaye daga Ghana zuwa manyan biranen kasar Sin.
Samuel Ablakwa ya kuma yaba wa masu zuba jari na kasar Sin kan rawar da suke takawa na aiwatar da ayyuka masu kawo sauyi a fadin kasar. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp