Rahotanni na nuna cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya, ta bunkasa matuka
Mai taimakawa ministan kasuwanci na kasar Sin Chen Chunjiang, ya bayyana a yayin wani taron manema labarai cewa, cinikayyar hajoji da kasar Sin ke yi da kasashen dake cikin wannan shawara, ya ninka daga dalar Amurka tiriliyan 1.04 a shekarar 2013 zuwa dalar Amurka tiriliyan 2.07 a shekarar 2022, karuwar kashi 8 cikin 100 a shekara.
Ya bayyana cewa, ya zuwa karshen shekarar 2022, kamfanonin kasar Sin sun zuba jarin da ya kai dalar Amurka biliyan 57.13 a yankunan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a kasashen dake cikin shawarar, inda suka samar da guraben ayyukan yi kusan dubu 421 ga mazauna yankunan.
A shekarar 2013 ce, kasar Sin ta gabatar shawarar ziri daya da hanya daya.(Ibrahim)