A jiya ne, aka gudanar da taron karawa juna sani tsakanin kamfanonin yawon shakatawa na kasashen Masar da Sin, da masu kula da yawon bude ido na kasar Masar a birnin Alkahira, domin tattauna hanyoyin kara yawan harkokin yawon bude ido a tsakanin kasashen biyu.
Da yake jawabi a yayin taron, ministan al’adu da yawon shakatawa na kasar Sin Hu Heping, ya ce kasashen Sin da Masar sun shahara a duniya, kuma muhimman wuraren yawon bude ido na juna.
Ministan ya kara da cewa, yana fatan kara karfafa mu’amala da hadin gwiwa tsakanin Sin da Masar a fannin yawon bude ido da kuma kayayyakin tarihi.
A nasa jawabin, ministan yawon bude ido da kayayyakin tarihi na kasar Masar, Ahmed Issa ya bayyana cewa, kasarsa na fatan hada kai tare da kasar Sin, da ma sa ran samun saurin bunkasuwar yawon shakatawa da musayar fasahohi na tarihi a tsakanin kasashen biyu.(Ibrahim).