Sakatariyar kasuwancin Amurka Gina Raimondo ta bayyana a yayin tattaunawa da manema labarai a kwanan nan cewa, motoci a yau sun kasance kamar “wayoyin salula na Apple masu taya” da ke iya tattara bayanai da yawa. “Idan akwai motocin kasar Sin miliyan 3 akan titunan Amurka, Beijing na iya sa su daina aiki a lokaci guda.” A yayin taron manema labarai a yau 4 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana cewa wadannan kalamai labaran karya ne, wadanda suka kasance alamar siyasantar da batutuwan tattalin arziki da cinikayya. Bisa wannan tunani, shin ya kamata kasar Sin ta kara damuwar cewa Washington za ta iya ba da damar watsa bayanan daruruwa miliyoyi da ke cikin wayoyin salular Apple wadanda Sinawa ke amfani da su zuwa ga Amurka ko kuma kashe wayoyin a lokaci guda?
Ban da wannan kuma, dangane da furucin da jakadan Amurka a kasar Sin Nicholas Burns ya yi a baya-bayan nan game da kasar Sin, Mao Ning ta bayyana cewa, kalaman na Amurka ba gaskiya ba ne, kuma ba sa da ma’ana, kuma Sin ta yi tir da hakan. Kasar Sin na adawa da yin amfani da takara wajen ayyana dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka. (Yahaya)