Tun daga ranar Talata 18 ga wata zuwa Alhamis 20 ga watan nan na Nuwamba, sojojin Sin da na Amurka sun gudanar da taron rukuni na biyu na aiki, da kuma taron shekara-shekara na tsarin tattauna tsaron aikin soja kan teku tsakanin Sin da Amurka na 2025, a jihar Hawaii ta Amurka.
Bisa jagorancin muhimmiyar matsaya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, bangarorin biyu sun yi musayar ra’ayoyi bisa daidaito, da girmama juna yayin taron, sun kuma yi musayar ra’ayoyi masu inganci kan yanayin tsaron teku, da na sama tsakanin Sin da Amurka. Bangarorin biyu sun amince cewa, taron tsarin tattauna tsaron aikin soja kan teku na Sin da Amurka, yana taimaka wa bangarorin biyu wajen shawo kan hadari da rikici. A sa’i daya kuma, kasar Sin ta bayyana cewa, za ta yi adawa da duk wani mataki da ka iya kawo barazana ga ikon mulkin kan kasar, da tsaronta, bisa fakewa da ‘yancin zirga-zirga a ruwa da sararin sama. (Safiyah Ma)














