ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Wasu Mahukunta Ke Amfani Da Muƙamansu Wajen Musguna Wa Al’umma

by Rabi'at Sidi Bala and Sulaiman
10 months ago
Nijeriya

Shafi ne da ya saba zaƙulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda wasu mutanen suke kasancewa ya yin da idan suka taka wani matsayi ko suka samu wani ci gaba/mukami, suke takurawa na kasa da su har su manta da mutuntawa ko darajantawa. Yayin da wasu kuma suke amfani da wannan damar wajen bullo da matsaloli ga wasu, dan kawai su yi yunkurin neman taimako gare su, su kuma su nemi wani abu gare su wato dai ‘ban gishiri na baka manda’. Hakan na faruwa a makarantu, ko wajen aiki da sauransu.

Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu. Ga dai bayanan nasu kamar haka:

 

ADVERTISEMENT

Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:

Eh, hakika hakan yana faruwa, amma a lokuta da dama mutunan dake da irin wannan hali za a same su da karancin ilimi, domin duk mai ilimi ya san darajar dan’adam musamman abokin aikin sa, sannan kuma mai ilimi ya san mulki ko daukaka wata aba ce ta lokaci don haka za ka ga yana mutunta mutane. Shawara ga masu irin wannan hali ya kamata su sani mulki ko daukaka wani abu ne na lokaci kuma Allah ne yake bada su, ita kuma kyakkyawar mu’amula wata abace da har bayan rayuwar ka zata amfane ka, don ya kamata mu guji wannan hali.

LABARAI MASU NASABA

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

 

Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rabo, Jihar Kano:

Akwai ajizanci da kuma dabi’ar ‘yan Nigeria. Hakan shi ne yake haifar da ‘yan baya suma su yi haka da zarar sun sami dama. Sharawata a nan ita ce mu rika tunawa da cewa kafin mu zama wasu, ko iyayenmu ko ‘yan uwanmu su zo wannan matsayin ko samun damar tofa an yi dubbannai kafin mu. Sannan haka nan gaba za a sami wasunmu sannan muna tuna cewa zamu mutu kuma a can (lahira) dukkanmu daya muke sai wadanda sukafi jin tsoron Allah dakuma aikata ayyukan alkhairi don haka mu gyara mu’amalamu da kowa basai wane da waneba domin bamusan karshen rayuwar kowaba. Allah kasa mudace.

 

Sunana Muktari Sabo, Jahun Jihar Jigawa:

Tabbas yana faruwa idan mutum ya taka wani mataki sai ya manta mafari har ya rinknga yin wasu abubuwa wa abokanan aikinsa na baya. Girman kai da mantuwa suke jawo hakan domin daya na tuna kafin ya hau wannan matakin, da yawa sun hau sun tafi da bai yi abin da bai kamata ba hakan tana yawan faruwa ne ga mutane masu son nuna izza da rashin sanin ya kamata, amma idan ba haka ba ai abokin aikinka kome ka zama ai za ka mutunta shi.

 

Sunana Yasar Saleh, Zareku Miga, Jihar Jigawa:

Hakan rashin adalci ne da nuna dagawa da rashin iya mu’amula. Kuma hakan na faruwa ne ta hanyar amfani da jahilcin mutane shi ya sa ake musu barazana, ake musu fin karfi da danniya. Hanyar da za a bi wajen hana wannan danniya ita ce samar da ilimi ga al’umma da kyautata mu’amula.

 

Sunana Princess Fatima Mazadu, Jihar Gombe:

Eh, ai shi dama mai kudi dan’uwansa mai kudi ne kawai mai daraja, amma talaka ai ba wansa ne, wanda ya fi raina wa wayo, kuma ta wani bangaren wasu sukan dubi canjin da ya same su ne a matsayin matakala na kaskantar da na kasa da su ko wadanda suka zar ce a baya tunda suke da mukami da dukiya, sukan kuntata musu ne saboda damar da suka samu, mafi akasarin matsalolin basu wuce na maida yaran talakawa bayinsu, matan muma matan banzansu na sharholiya ya yin da suka nemi taimako a wurinsu take suke bullo da tasu bukatar mai kwadayi ya afka wa mara kwadayi talauci ta yi yadda take so da shi ko Allah ya nuna ikonsa. Gaskiya ya fi faruwa a ma’aikata in mace ta je neman aiki a nuna mata zallar kwadaituwa da ita ko ta rasa wannan damar, makaranta malamai mafi akasari suna amfani da wannan damar ne wurin guje musu ‘carry ober’ su lalalatasu abisa agansu da ‘carry ober’ gara komai ya faru su fita ko da ‘pass’. Gaskiya gadara da iko na wurin mai arziki ko mai mukami wanda a kankanin lokaci talaka zai kaskanta dolenshi a karkashinsu.

 

Sunana Hafsat Sa’eed, Neja:

Mafi akasari mutane idan suka samu wata dama sai su sai su dauki wadanda suka tashi tare ko suka yi mu’amula tare sai suka kamar su sun fi karfinsu, ko kuma suna jiran su je su nemi wani abu a wajensu, amma ba dukka bane aka taru aka zama daya ba. Suna da yawa, kaso casa’in cikin dari za ka same su da wannan halin. Wannan ba hali bane me kyau indai kana da mutunci da daraja me kyau, duk abin da ya zo maka ba zai yu ace ka wulakanta na kusa da kai ko na kasa da kai, ko kuma ka rika kallonsa da raini. Mafi akasari yadda zuciyoyi suke a wajen mutane wasu na ganin kamar burgewa ne , ni a nawa ganin hakan ba burgewa bane. Domin Allah yana iya juya al’amarinsa ya mayar da kai ba kowa ba, wanda ka ke rainawar Allah ya daga shi.

 

Sunana Abba Abubakar Yakubu daga Jos, A Jihar Filato:

Darasin wannan mako yana da matukar muhimmanci, wajen tunatarwa gare mu duka, akan jarabawar rayuwa. Babu shakka arziki da daukaka jarabawa ce da Allah ya yi wa bawa, don ya ga yadda zai karbeta, kuma ya yi amfani da ita. Abin da addini ya koya mana shi ne, idan Allah Ya yi maka wata baiwa ta arziki ko ta daukaka, tamkar an bai wa dukkan jama’ar da ke tare da kai ne. Abin da hakan ke nufi shi ne, ka yi amfani da wannan dama da ka samu wajen kyautata musu, tausaya musu, da kuma tallafawa rayuwarsu. Kada arzikin da ka samu yayin zama dama ta nisantar ‘yan’uwanka, da abokanka, musamman waɗanda ku ka taso tare, ku ka yi wahala tare. Kada ka wulakanta su, ko ka rika yi musu kallon kaskanci. Domin rabonsu ne a hannunka, kuma addu’ar wani daga cikin su ta sa Allah tausaya maka har ya ba ka wannan baiwar da ka ke takama da ita.

Al'umma
Rabi'at Sidi Bala
+ posts Bio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Alaƙata Da Adamu Zango Ta Bunƙasa A Kannywood —Jarumi Ibrahim Sodangi 
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?
Al'umma
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

MASU ALAKA

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?
Taskira

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

September 5, 2026
Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?
Taskira

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

August 29, 2026
Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?
Taskira

Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?

July 25, 2026
Next Post
Tsaro: Gwamnatin Kebbi Ta Bayar Da Umarnin Rufe Duk Makarantun Sakandare Da Jami’o’in Jihar

Tsaro: Gwamnatin Kebbi Ta Bayar Da Umarnin Rufe Duk Makarantun Sakandare Da Jami’o’in Jihar

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.