Kasar Sin na matukar adawa da haramta amfani da kirkirarriyar basira ta DeepSeek da gwamnatin Amurka ta yi a ranar Talata, biyo bayan rahoton da kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar na cewa, ma’aikatar cinikayya ta Amurka ta haramtawa ma’aikata amfani da DeepSeek kan na’urorin da gwamnati ta samar musu.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin a ko da yaushe tana adawa da zuzuta batun tsaron kasa fiye da kima, da siyasantar da batutuwan da suka shafi tattalin arziki, cinikayya da fasaha. Mao ta kara da cewa, kasar Sin za ta kare hakkoki da muradun kamfanonin kasar Sin. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp