• English
  • Business News
Tuesday, October 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Na Ci Gaba Da Ingiza Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

bySulaiman
1 year ago
inDaga Birnin Sin
0
Sin Na Ci Gaba Da Ingiza Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

{"ARInfo":{"IsUseAR":false},"Version":"1.0.0","MakeupInfo":{"IsUseMakeup":false},"FaceliftInfo":{"IsChangeEyeLift":false,"IsChangeFacelift":false,"IsChangePostureLift":false,"IsChangeNose":false,"IsChangeFaceChin":false,"IsChangeMouth":false,"IsChangeThinFace":false},"BeautyInfo":{"SwitchMedicatedAcne":false,"IsAIBeauty":false,"IsBrightEyes":false,"IsSharpen":false,"IsOldBeauty":false,"IsReduceBlackEyes":false},"HandlerInfo":{"AppName":2},"FilterInfo":{"IsUseFilter":false}}

A watannin 6 na farkon shekarar bana alkaluma sun tabbatar da cewa tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da farfadowa da bunkasa bisa daidaito. Kaza lika, a ranar 16 ga watan nan ma asusun IMF ya fitar da sabon hasashen bunkasar tattalin arzikin duniya, wanda ya nuna yiwuwar bunkasar tattalin arzikin kasar Sin da kaso 5 bisa dari a bana, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 0.4 bisa dari kan hasashen da asusun ya fitar a watan Afrilun da ya gabata.

Masharhanta na cewa wannan hasashe na bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, zai samar da karsashi na dogon lokaci ga farfadowa, da bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya. IMF dai ya amince cewa bunkasar tattalin arzikin kasashen Asiya masu samun saurin ci gaba ciki har da Sin, shi ne jigon bunkasar tattalin arzikin duniya, musamman a gabar da tattalin arzikin Sin ke kara habaka ta fuskar yawa da kuma inganci.

  • Gamayyar Ƙungiyoyin Matasan Arewa Da Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Sun Buƙaci Matasa Su Kaucewa Shiga Zanga-zanga
  • Wasu Ɓata-gari Na Iya Amfani Da Zanga-zanga Domin Tada Zaune Tsaye – Minista

Alkaluma sun nuna cewa a wa’adin watanni 6 na farkon shekarar nan ta 2024, ma’aunin bunkasar tattalin arzikin kasar Sin na GDP ya karu da kaso 5 bisa dari, inda darajarsa ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 61.7, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 8.49. Tsakanin wannan wa’adi, adadin sayayyar kayayyakin bukatun al’umma a kasar ta Sin, da hidimomi masu nasaba da hakan duk sun karu, yayin da jarin da ake kara zubawa a fannin samar da ababen more rayuwa ya daga da kaso 5.4 bisa dari kan na makamancin lokaci na bara.

Labarai Masu Nasaba

Habakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu   

Karamin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka

Karin sassan dake bunkasa sun hada da na sarrafa hajoji a masana’antu, da cinikayyar waje, wadda a wannan wa’adi darajarta ta kai kudin Sin yuan tiriliyan 21.2. Bisa dukkanin shaidu, tun daga mahanga ta kusa har zuwa tsawon lokaci mai zuwa, sassan tattalin arzikin kasar Sin za su ci gaba da bunkasa, yayin da kasar ke kara samun bunkasuwa mai inganci.

Idan an yi duba na tsanaki, abu ne mai sauki a gano dalilan da suka haifar da wannan nasara da kasar Sin ke samu. Ga misali bunkasar sarrafa hajojin masana’antu masu kunshe da fasahohin zamani, da sarrafa hajoji ba tare da gurbata muhalli ba sun taka rawar gani wajen ingiza tattalin arzikin kasar Sin.

Kaza lika fannin bunkasar sabbin fannonin samar da hajoji irin su kayayyaki masu amfani da kirkirarriyar basira, da fasahar sarrafa manyan bayanai, da hidimomin sayyaya ta yanar gizo, dukkaninsu sun baiwa kasar damar cin karin gajiya.

Har ila yau, kwazon kasar Sin na zurfafa gyare-gyare a dukkanin fannoni ya samar da sabon karfi na ingiza ci gaba mai inganci, da nasarar matakan zamanantarwa irin ta Sin. Masana da masharhanta sun yi imanin cewa tattalin arzikin kasar Sin zai sauya daga tsohon matakinsa zuwa sabon salo mai inganci, karkashin manufofin zurfafa gyare-gyare da kara bude kofofin kasar ga kasashen waje.

Yayin da ake fatan cimma nasarar hakan, kasar Sin ta wanzar da alakar cinikayya da sama da kasashen duniya da yankuna 140, wanda hakan ya sanya jimillar hada hadar hajojin kasuwancinta da kasashen waje ya kai matsayin farko a duniya cikin shekaru 7 a jere.

Bugu da kari, shawarar “ziri daya da hanya daya” ko BRI da kasar Sin ta gabatar ita ma na taka rawar ganin wajen dinke kasar da sauran sassan duniya ta fuskar cimma moriyar juna, inda kawo yanzu sama da kasashen duniya 150, da hukumomin kasa da kasa 30 suka shiga wannan shawara mai riba.

Masharhanta na ganin wannan ci gaba da Sin ke samu, dama ce ta musamman ga daukacin duniya ta morewa fasahohin Sin, da cimma moriyar juna, ta yadda dukkanin sassan duniya za su hada gwiwa domin a gudu tare a tsira tare. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare
Sulaiman

Sulaiman

Related

Habakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu   
Daga Birnin Sin

Habakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu   

21 hours ago
Karamin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka
Daga Birnin Sin

Karamin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka

22 hours ago
Nazari Ya Gano Falalen Dutse Na Yanki Mai Nisa A Duniyar Wata Ya Fi Tsananin Sanyi Fiye Da Na Yanki Na Kusa
Daga Birnin Sin

Nazari Ya Gano Falalen Dutse Na Yanki Mai Nisa A Duniyar Wata Ya Fi Tsananin Sanyi Fiye Da Na Yanki Na Kusa

23 hours ago
Next Post
CMG Ta Fitar Da Ma’aunin Watsa Labarai Kai Tsaye Na Wasannin Olympics Na Paris Da Kuma Kafa Studiyonta A Gaban Eiffel

CMG Ta Fitar Da Ma’aunin Watsa Labarai Kai Tsaye Na Wasannin Olympics Na Paris Da Kuma Kafa Studiyonta A Gaban Eiffel

LABARAI MASU NASABA

Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane

Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane

October 7, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu

October 7, 2025
Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

October 7, 2025
Tsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan Bindiga

Tsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan Bindiga

October 7, 2025
Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya

Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya

October 7, 2025
Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

October 7, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026

October 7, 2025
Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

October 6, 2025
Kada Ku Yi Sanadiyar Rugujewar Matatar Mai Ta Dangote – Shettima Ga PENGASSAN 

Kada Ku Yi Sanadiyar Rugujewar Matatar Mai Ta Dangote – Shettima Ga PENGASSAN 

October 6, 2025
Habakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu   

Habakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu   

October 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.