Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin na fatan ganin Amurka ta yi watsi da daukar matsaya biyu, ta fuskanci matsalolin ta na cikin gida, musamman kalubalen amfani da karfin tuwo, da wariya da jami’an ‘yan sanda ke nunawa fararen hula.
Mao, wadda ke amsa tambayar da aka yi mata, yayin taron manema labarai a Litinin din nan, game da kisan wani Ba’amurke bakar fata a baya bayan nan, ta ce ya kamata mahukuntan Amurka su dauki kwararan matakan kaucewa sake aukuwar wannan lamari.
Game da tambayar da aka yi mata, kan ziyarar sakataren wajen Amurka Antony Blinken a Sin kuwa, Mao Ning ta ce ba zai yiwu Amurka ta rika tsoma baki a harkokin gidan kasar Sin, tare da gurgunta moriyar kasar, a lokaci guda kuma ta rika batun tattaunawa da hadin gwiwa da Sin ba.
Har ila yau, game da zargin da Amurka ke yiwa wasu kamfanonin kasar Sin, cewa wai suna tallafawa kasar Rasha kuwa, Mao Ning ta sake jaddada cewa, Sin ba za ta zuba ido kawai, ko ta kara ruwa wutar yanayin da ake ciki, ko yunkurin cin gajiya daga rikicin Ukraine ba. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)