• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Na Taka Rawar Gani Wajen Inganta Dunkulewar Duniya Da Kyautata Cinikayyar Kasa Da Kasa

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

Idan har da gaske ake son a ciyar da duniya gaba, to hadin gwiwar siyasa da tattalin arziki, da hadin gwiwa a fannin kirkire-kirkire da inganta kwararrun masana’antu na kasa da kasa sun zama wajibi don tunkarar hadarin kenkene kasuwanci ta hanyar sanya takunkumi, da gurbacewar muhalli, da rikice-rikicen tattalin arziki, da rugujewar tsarin samar da kayayyaki a duniya. Kana, karfafa amincewa da juna yayin hadin gwiwa don shawo kan wadannan kalubalolin na da matukar muhimmanci.

Domin ba da shawara game da yadda za a tunkari wadannan matsalolin, Firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya (WEF) na shekarar 2024 da aka gudanar a Davos, ya kuma gabatar da muhimmin jawabi a ranar 16 ga wannan wata, kasancewar kasar Sin a gun taron ya nuna cewa, a shirye take ta ci gaba da taka rawar gani, wajen inganta hadin gwiwar tattalin arzikin kasa da kasa da kuma tunkarar matsalolin duniya.

  • Sin Ta Yaba Da Kokarin Kasashe ‘Yan Ba Ruwanmu Wajen Ciyar Da Zaman Lafiya Gaba A Duniya
  • Yin Gyare-Gyare Da Bude Kofa Dabara Ce Ta Raya Fuzhou

Yunkurin da kasar Sin ta yi kan muhimmancin ra’ayin bangarori daban-daban ya ba da tabbacin cewa gudummawar da take bayarwa na ciyar da bil’adama gaba. A cikin shawarwarin da firaministan ya gabatar, ya yi kira da a daidaita manufofin tattalin arziki, da inganta kwararrun masana’antu na kasa da kasa, da hadin gwiwa a fannin kirkire-kirkire, da hadin gwiwa a fannin raya koren muhalli, da hadin gwiwa tsakanin sassan duniya, yayin da ya jaddada aminci tsakanin shugabannin kasashen duniya.

Baya ga zaman lafiya da ci gaban kasar Sin, ba shakka kasashen duniya suna sa ido kan irin gudummawar da kasar Sin ke bayarwa wajen kara tabbatar da dunkulewar tattalin arzikin duniya. Kamar yadda Okonjo-Iweala, babbar darektar hukumar cinikayya ta duniya (WTO) ta ce a gefen taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya da aka gudanar a Davos, yayin da take bayyana muhimmiyar rawar da kasar Sin ke takawa wajen habaka cinikayyar duniya da kuma ci gaban tattalin arzikin duniya, “Duk abin da ya faru da kasar Sin yana yin tasiri ga duniya, hakan ya sanya taka rawar ganin tattalin arzikin kasar Sin ya kasance maslahar kowa da kowa.”

La’akari da taken dandalin tattaunawar tattalin arziki na duniya na 2024 wato “karfafa amincewa” wanda ya jaddada sauke nauyi, da bude kofa, da daidaita gibi tsakanin kasashe masu tasowa da masu ci gaba, da daidaito don jaddada amincewa da juna yayin da ake warware matsalolin duniya kamar sauyin yanayi, rikice-rikicen shiyya-shiyya, da ci gaban kirkirarriyar basira wato AI, da ingancin tsarin samar da kayayyaki a duniya da farfado da tattalin arziki duk suna dogaro ne ga kwarin gwiwa da aminci tsakanin kasashe masu tasowa da ma masu ci gaba.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

Dole ne dandalin na WEF ya zama kafa mai samar da sauki ga hada-hadar kasuwanci a duniya da kuma kawar da shingayen cinikayya, da kiyaye tsarin samar da kayayyaki. Kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan inganta dunkulewar duniya da manufar dandalin WEF ta cire shingaye daga cinikayyar kasa da kasa. (Muhammed Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

November 6, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST
Daga Birnin Sin

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025
Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya
Daga Birnin Sin

Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

November 6, 2025
Next Post
An Kammala Bitar Wasan Kwaikwayo Karo Na Biyu Na Shirye-Shiryen Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Na 2024 

An Kammala Bitar Wasan Kwaikwayo Karo Na Biyu Na Shirye-Shiryen Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Na 2024 

LABARAI MASU NASABA

An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

November 7, 2025

Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho

November 7, 2025
Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

November 7, 2025
Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 

Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 

November 7, 2025
An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

November 6, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025
Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

November 6, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

November 6, 2025
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.