A yayin taron manema labaru da aka saba yi a yau Litinin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi bayani kan shawarwarin da aka yi tsakanin jami’an ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin da na Japan. Jami’ar ta ce bangaren kasar Sin ya bayyana matsayarsa, da tsantsar adawarsa ga yunkurin kasar Japan, na zubar da ruwan dagwalon nulikiyar Fukushima a cikin teku, ya kuma bukaci Japan da kada ta bi ra’ayinta ba tare da yin la’akari da komai ba, kan batun zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku.
Mao Ning ta ce, shugaban sashen kula da harkokin Asiya na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Liu Jinsong, ya gudanar da shawarwari karo na uku, a bana tare da shugaban ofishin kula da harkokin Asiya da Oceania a ma’aikatar harkokin wajen kasar Japan Takehiro Funakoshi, a birnin Tokyo a ranar 22 ga watan nan, kuma an zurfafa shawarwarin bisa gaskiya, an kuma hadu da sabani a wasu bangarori, tare da dacewa a wasu sassa.
Daga karshe bangarorin biyu sun yi imanin cewa, ya kamata a dauki bikin cika shekaru 45 da kulla yarjejeniyar zaman lafiya, da abokantaka ta Sin da Japan, a matsayin wata dama ta ci gaba da tuntubar juna a dukkan matakai, da karfafa hadin gwiwa a aikace, da mu’amala a fannin al’adu.
Bangarorin biyu sun kuma yi musayar ra’ayi, kan batutuwan da suka shafi kasa da kasa da na shiyyoyi, inda suka amince da ci gaba da gudanar da irin wannan shawarwari. (Mai fassara: Bilkisu Xin)