Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya sake bayyana matsayin kasarsa game da zubar da dagwalon ruwan nukiliyar Japan cikin teku, yayin taron manema labarai da aka saba yi na yau Jumma’a, inda ya bukaci bangaren Japan da kada ya yi amfani da rahoton hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA, a matsayin izinin gudanar da wannan aiki.
Rahotanni sun nuna cewa, Darakta Janar na hukumar IAEA Rafael Mariano Grossi, ya ce, kwararrun kasa da kasa da ke da ruwa da tsaki wajen nazari, da tantance gurbataccen ruwa na Fukushima a Japan, suna da sabanin ra’ayi game da cikakken rahoton tantancewar.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Wang Wenbin ya ce, “Wannan ya sake nuna cewa, hukumar ta yi gaggawar fitar da rahoton, wanda bai samu amincewar dukkanin ra’ayoyin kwararrun da ke gudanar da aikin tantancewar ba, kuma sakamakon ya dace ne kawai da amincewar bangare daya, bai kuma kawar da damuwar kasashen duniya game da shirin kasar Japan, na zubar da dagwalon ruwan nukiliya cikin teku ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp