Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya ce Sin na fatan majalisar za ta mai da hankali ga batun rarraba kudade, da lura da matsalolin jin kai da ba a samar musu da isassun kudaden magancewa, da daukar matakai masu dogon zango, domin magance wadannan matsaloli, da zage damtse wajen cimma daidaito a fannin samar da tallafin shawo kan matsalolin jin kai bisa adalci.
Geng Shuang ya yi kiran ne a Juma’ar nan, yayin taron tattaunawa don gane da ayyukan jin kai na shekarar 2024, karkashin hukumar lura da tattalin arziki da zamantakewa ta MDD. Ya ce, har kullum kasar Sin na dora matukar muhimmanci ga ayyukan da suka shafi jin kan bil Adama, tana samar da babban tallafi ga kasashe masu tasowa, karkashin kafofin hadin gwiwar kasashe daban daban, don samar da tallafin gaggawa, da farfadowa bayan ibtila’i, da sake gina yankuna. Kaza lika, Sin din na bunkasa matakanta na kandagarkin aukuwar bala’u da dakushe mummunan tasirinsu. (Saminu Alhassan)