Yau Laraba, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum.
Game da taron da aka yi tsakanin Sin da Cambodia da Thailand a yau a birnin Shanghai na kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana cewa, an gudanar da taron cikin sahihanci. Kasashen Cambodia da Thailand sun nanata wa kasar Sin kudurinsu na cimma matsaya kan tsagaita bude wuBayanin da ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya yi a baya-bayan nan game da hasashe kan tattalin arzikin kasar Sin cikin shekaru biyar masu zuwa ya jawo hankalin duniya sosai. Kuma sakamkon binciken jin ra’ayoyin jama’a da CGTN na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya yi a tsakanin masu bayyana ra’ayoyi 47,000 a kasashe 46 daga shekarar 2023 zuwa 2025, ya nuna jama’ar sun nuna yakini game da karfi da juriyar tattalin arzikin kasar Sin.
- Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
- Matatar Mai Ta Fatakwal Ba Ta Siyarwa Ba Ce – NNPC
Binciken ya nuna cewa, yawancin masu bayyana ra’ayoyin daga sassan duniya suna da kyakkyawan fata ga tattalin arzikin kasar Sin wajen samun bunkasa mai kyau a dogon lokaci, inda amincewarsu ta kai kashi 74.7 bisa dari, da 81.3 bisa dari, da kuma 81.9 bisa dari cikin shekaru uku a jere.
Binciken da aka yi a bana ya kuma nuna cewa, masu bayyana ra’ayoyin suna da kwarin gwiwa game da samun damammaki masu kyau a kasuwar Sin a cikin yanayin kasa da kasa mai sarkakiya da tashe-tashen hankula. A cikinsu akwai kashi 79.8 bisa dari da suka bayyana cewa, babbar kasuwar Sin ta ba da muhimman damammaki ga kasashen da suke gudanar da kasuwanci a ciki.(Safiyah Ma)ta, tare da nuna godiya da kyakkyawar rawar da kasar Sin ke takawa wajen saukaka halin da ake ciki. Guo Jiakun ya kuma bayyana cewa, kasar Sin na ci gaba da aikin tukuru don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Dangane da tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka da aka gudanar a kwanan nan, Guo Jiakun ya bayyana cewa, ana fatan bangaren Amurka zai yi aiki tare da Sin wajen amfani da tsarin tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, don sa kaimi ga bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka cikin kwanciyar hankali.
Dangane da batun Falasdinu kuwa, Guo Jiakun ya ce, “manufar kafa kasashe biyu” ita ce hanya daya tilo ta hakika ta warware matsalar Falasdinu, kuma kasar Sin tana goyon bayan al’ummar Falasdinu wajen kafa kasa mai cin gashin kanta.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp