Hukumar kula da ayyukan sama jannati ta kasar Sin ko CMSA a takaice, ta ce tuni aka fara shirye shirye, na aikewa da Sinawa duniyar wata. CMSA ta ce ana fatan saukar Sinawa a doron duniyar wata nan zuwa shekarar 2030.
Tuni dai aka fara tsara ayyukan bincike, da samar da kayayyakin aiki. Kaza lika ana sa ran amfani da cibiyar harba kumbuna ta Wenchang dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin, a matsayin wurin da za a gina dandalin aiwatar da wannan muhimmin aiki. (Mai fassara: Saminu Alhassan)