Ma’aikatar raya al’adu da yawon bude ido, ta fitar da wasu jerin matakai na bunkasa hade sassan harkokin raya al’adu da yawon shakatawa, ciki har da farfado da nune nunen al’adun gargajiya na “opera” da fasahohin gargajiya.
Ministan ma’aikatar Hu Heping, ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin taron jami’an hukumomin da lamarin ya shafa, inda ya yi kira da su kara azama wajen aiwatar da matakan hade sassan hada hadar raya al’adu da yawon shakatawa yadda ya kamata, bisa inganci, ta yadda hakan zai ingiza sabon ci gaba da kuzari a fannonin biyu.
Yayin taron na jiya, an bayyana cewa, tsare tsaren ma’aikatar sun kunshi tallafawa ‘yan wasan al’adun gargajiya na “opera”, wasan dake daf da bacewa, tare da farfado da sauran al’adun gargajiya na fasahohin kasar Sin, da bunkasawa, da karewa tare da amfani da abubuwan al’adu da aka gada daga kaka da kakanni, da karfafa tare da kiyaye abubuwan al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba, da bunkasa fasahohin kiyaye dakunan karatu dake dukkanin sassan kasar, da sauran ayyuka da za a gudanar cikin wannan shekara ta 2023.
Har ila yau, ma’aikatar raya al’adu da yawon shakatawa ta Sin, ta ce ta tanadi wasu matakai da dama na farfado da yawon bude ido, ciki har da bunkasa harkokin manyan lambunan raya al’adu na kasa, kamar na rawayen kogi, da na babbar ganuwar kasar Sin, tare da yayata sabon salon tafiye tafiya, kamar na yawon shakatawa a yankunan karkara, da bulaguro cikin rukunonin mutane. (Saminu Alhassan)