Mataimakin wakilin Sin na dindindin a MDD Geng Shuang ya ce, ana samun karuwar yadda wasu kasashe ke nuna son kai da kuma babakere, wanda ke kawo cikas ga ka’idojin shari’a na duniya, kamar daidaiton ‘yancin kai da kaucewa tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe.
Geng Shuang ya bayyana haka ne jiya Alhamis a gun taron kwamiti na shida na babban taron MDD na 80, inda ya kara da cewa, ana kara fuskantar hadarin siyasantar da tsarin shari’a da kuma amfani da shi a matsayin makami, lamarin dake haifar da kalubale ga bangaren shari’a na duniya.
Duba da hakan, Sin ta gabatar da shawarwari shida game da “tsarin shari’a a cikin gida da ma duniya baki daya”:
Na farko, manufofi da ka’idojin kundin mulkin MDD su kasance tushen ka’idojin dangantakar kasa da kasa, kuma jigon tsarin shari’a na duniya.
Na biyu, dole ne dokokin duniya su mutunta bambancin al’adu da tsare-tsaren shari’a na kasashen duniya, tare da tabbatar da cewa dukkannin kasashe na da matsayi iri daya, kuma ya zama dole a karfafawa kasashe masu tasowa gwiwar yin magana.
Na uku, daidaiton ‘yancin kai ya kasance tushen shari’a ta zamani a duniya.
Na hudu, nuna biyayya ga yarjejeniyoyin kasa da kasa, wata babbar ka’ida ce wajen aiwatar da shari’a a duniya, kuma dole ne dukkannin kasashe su cika alkawuransu bisa aminci da gaskiya.
Na biyar, dole ne kasashe su gaggauta tsara dokoki a sabbin fannonin da sabbin bangarorin tsaro, don samar da tsarin hadin gwiwa da shugabancin duniya a wadannan bangarori, ta yadda za su biya bukatu da kuma magance matsalolin da suka dace da bukatun kasashe.
Na shida, warware rikice-rikice ta hanyar zaman lafiya wata babbar ka’ida ce ta shari’ar duniya, kuma neman sulhu daya ne daga cikin hanyoyin da kundin mulkin MDD ta kayyade na magance rikice-rikice. (Amina Xu)