A yau ne, kasar Sin ta yi nasarar harba wani sabon tauraron dan adam zuwa sararin samaniya, daga cibiyar harba tauraron dan adam ta Jiuquan dake yankin arewa maso yammacin kasar.
An harba tauraron dan Adam mai suna, Yaogan-33 04, ta hanyar amfani da rokar Long March-4C da misalin karfe 4 da mintuna 15 na safe, agogon Beijing na kasar Sin, kuma ya shiga falaki kamar yadda aka tsara.
- Ra’ayin Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ta Bai Daya Na Tattaro Karfin Sauya Duniya
- ‘Yan Wasan Kasar Sin Sun Lashe Lambar Zinare Ta Farko A Gasar Wasannin Asiya Karo Na 19
Za a yi amfani da tauraron ne, wajen gudanar da gwaje-gwajen kimiyya, da binciken albarkatun kasa, da kididdigar yawan amfanin gona da aka samu, da rigakafin bala’i da aikin agaji.
Wannan shi ne karo na 489 da aka yi amfani da rokar Long March, wajen harba taurarin dan-Adam. (Ibrahim Yaya)