Shugaban tawagar Sin a kwamiti mai kula da harkokin jan damara da tsaro na babban taron MDD karo na 79, kana darektan sashen kayyade damara na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Sun Xiaobo ya gabatar da jawabi a muhawarar da aka yi a jiya Alhamis.
Sun ya ce, tunanin yakin cacar baka da ra’ayin fin karfi, munanan matakai ne dake jefa bil Adam cikin kangiya. Ba za a iya tabbatar da zaman lafiya da tsaron duniya ba, sai in an nace ga bin ra’ayin bangarori daban daban a duniya bisa adalci da zaman oda da doka, da ra’ayin tsaro mai dorewa dake shafar mabambantan bangarori dake hadin gwiwar kasa da kasa. Ya ce, hana amfani da murkushe makaman nukiliya da kafa wata duniya da babu makamashin nukiliya a cikinta, kana da kawar da barazanar makaman, ya dace da muradun daukacin bil Adam, kuma buri ne na duk fadin duniya. Sin ta yi kira da a tabbatar da hadaddiyar sanarwar da shugabannin kasashe 5 dake mallakar makaman nukiliya suka gabatar, don kaucewar yakin makaman nukiliya da gasar makamai. A matsayin mai sulhu a cikin wadannan shekaru 5, Sin za ta ci gaba da taka rawarta yadda ya kamata.
Ban da wannan kuma, Sin tana kalubalantar kasashe masu ruwa da tsaki da su daina bunkasa da jibge tsarin na’urorin kakkabo makamai masu linzami, da daina girka na’urorin kakkabo makamai masu linzami a tsakar zangonsu dake dab da kasashe dake da karfin makaman nukiliya. (Amina Xu)