A yau Laraba kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana cewa aikin gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa, a karshen kogin Yarlung Zangbo, aiki ne dake bisa ikon mallakar kasar Sin, kuma Sin din tana raya aikin don gaggauta samar da makamashi mai tsabta, da kyautata zaman rayuwar jama’ar wurin, da kuma tinkarar sauyin yanayi.
Guo ya ce, kasar Sin ta mai da hankali, da sauke nauyin dake wuyanta na amfani da albarkatun kogin da ya ratsa bangarenta da ma kasashen waje, kana tana da fasahohin gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa. An tsara aikin ne a kan karshen kogin Yarlung Zangbo bisa ma’aunin Sin mai nasaba da aiki, da gudanar da aikin tare da kiyaye muhalli, da magance aikin a muhimman wuraren halittu don tabbatar da tsarin yanayin wanzuwar halittu. An gina tashar don magance bala’i a kan kogin, ta yadda aikin ba zai yi wata illa ga yankin karshen kogin ba.
Guo Jiakun ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta yi hadin gwiwa tare da kasashen dake kan karshen kogin a fannonin sanar da yanayin kogin, da magance bala’i, da yaki da bala’i da sauransu, da kuma yin mu’amala da kasashen don ci gaba da yin hadin gwiwa da su, da kuma kawo moriya ga jama’arsu baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp