Sakataren zartaswa dake lura da yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD ko UNFCCC Simon Stiell, ya jinjinawa kokarin kasar Sin, bisa aiwatar da managartan matakan shawo kan mummunan tasirin sauyin yanayi.
Mr. Stiell, wanda ya yi wannan tsokaci a jiya Juma’a, yayin zantawa da tawagar kasar Sin a taro na 27, na kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD ko COP27, wanda ke gudana a birnin Sharm El-Sheikh na kasar Masar.
Stiell ya ce a wannan gaba da duniya ke fuskantar rikicin makamashi, Sin ta ci gaba da aiwatar da matakai masu inganci na shawo kan sauyin yanayi, ta kuma taka muhimmiyar rawa wajen ingiza kwazon da ake yi a fannin a matakin kasa da kasa.
Wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana wakilin musamman na Sin game da sauyin yanayi Xie Zhenhua, kuma jagoran tawagar Sin a taron na COP27, Zhao Yingmin, sun yi tattaunawa mai zurfi da Mr. Stiell, game da muhimman batutuwan da suka shafi ajandar taron na COP27. (Saminu Alhassan)