Mai rikon mukamin jakada a zaunanniyar tawagar kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya, Dai Bing, ya bayyana a jiya Litinin cewa, kasarsa tana maraba da gudanar da taron neman sulhu tsakanin al’ummomin kasar Libiya, da mara baya ga bangarori masu ruwa da tsaki don su yi kokarin samun sulhu, ta yadda za’a kirkiro yanayi mai kyau don warware matsala ta hanyar siyasa.
A yayin taron da kwamitin tsaron MDD ya shirya game da batun Libya, Dai ya ce, hanyar siyasa, ita ce mafita ta daidaita batun Libya.
Majalisar wakilan jama’ar kasar Libya, da kwamitin kolin kasar, duk sun bayyana niyyarsu ta farfado da shawarwari ba tare da wani jinkiri ba.
Kasar Sin tana maraba da hakan, ta kuma goyi bayan bangarori daban-daban su gudanar da zabe karkashin jagorancin MDD, don kawo karshen takun-sakar siyasar kasar. (Murtala Zhang)