A kwanakin baya ne MDD ta gudanar da wani taro na musamman dangane da yadda wasu kasashe ke nuna kyama ga addinin musulunci, inda ta jaddada wajibcin daukar kwararan matakai na yaki da nuna kyama da wariya da cin zarafin addinin musulunci.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a wannan rana cewa, ya kamata gwamnatin Amurka ta dauki matakai na zahiri don kawar da nuna kyama da addinin musulunci.
A dangane da fashewar bututun jigilar iskar gas na “Nord Stream” kuwa, Wang Wenbin ya ce, ya zama tilas kwararru su gudanar da cikakken bincike na hakika, ba tare da nuna son kai ba kan lamarin da kuma gudanar da bincike kan alhakin da ya dace.
Game da batun yankin Gabas ta Tsakiya, Wang ya ce, a matsayinta na aminiyar kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, kasar Sin ba ta da wani muradin nuna son kai a yankin, ba ta shiga cikin kananan rukunnai ba, tana mai da hankali kan daidaita batutuwa masu muhimmanci a siyasance, kuma har kullum ta kasance mai nuna adalci kuma mai shiga tsakani abin dogaro.
Dangane da taron koli na shugabancin demokuradiyya da Amurka za ta yi nan gaba kadan, Wang Wenbin ya bayyana cewa, taron da ake kira “kolin demokuradiyya” hakika ya sabawa tsarin demokradiyya.
Dangane da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Amurka da Birtaniya da Autraliya kan jiragen karkashin teku masu amfani da makamashin nukiliya, Wang Wenbin ya ce, kasar Sin na adawa da yadda kasashen Amurka da Birtaniya da Autraliya take tilastawa sakatariyar hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA ta amince da hadin gwiwarta kan jiragen ruwan karkashin tekun masu amfani da makamashin nukiliya. (Mai fassarawa: Ibrahim)