Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta ce za a fara yi wa wasu muhimman rukunonin jama’a allurar riga kafin COVID-19 a lokacin hunturu da bazara.
Yayin wani taron manema labarai, Cui Gang, jami’in sashen takaita yaduwar cututtuka na hukumar, ya ce a wani shirin bayar da riga kafi mai matakai 2, a mataki na farko, za a fara ba da riga kafin ga wasu rukunonin da suka hada da wandanda ke lura da kayayyakin sanyi da ake shigo da su kasar da ma’aikatan wuraren bincike a tashoshin ruwa da na bangaren kebe wadanda suka kamu da bangaren sufurin jiragen sama da na motocin haya da kasuwannin kayan gwari da ma’aikatan lafiya da masu takaita yaduwar cututtuka.
Cui Gang, ya ce shirin bayar da riga kafin zai kuma shafi wadanda ke shirin zuwa aiki ko karatu a kasashe da yankunan da suka fi fuskantar barazanar yaduwar cutar da kuma wadanda ke kan matsakaicin matakin barazana.
A cewarsa, wannan zai taimaka wajen ragewa kasar matsi ta fuskar kandagarki da taikata shigo da cutar, da kuma rage hadarin barkewarta a kasar.
Riga kafin na kasar Sin ya shiga matakin gwaji na karshe, inda ake gwajin nau’o’i 5 kan mutane. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CRI Hausa)