A yau Juma’a ne babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta sanar da cewa, tun daga gobe Asabar, Sin za ta fara karbar kaso 125 bisa dari na harajin fito kan kayayyakin Amurka da ake shigarwa kasar.
Sanarwar dai ta biyo bayan sanarwar da Amurka ta fitar, ta yi wa kayayyakin da ake shigarwa kasar daga Sin karin harajin ramuwar gayya, na kaso 125 bisa dari. Hukumar ta ce, mummunan karin harajin da Amurka ta yi, ya sabawa dokokin tattalin arziki na kasa da kasa, da dukkanin ka’idojin cinikayya, da ma hankali, kuma hakan wani mataki ne na nuna fin karfi daga bangare daya, da kuma yunkurin yin matsin lamba.
- CMG Ya Kaddamar Da Nuna Fina-Finai Da Shirye-Shiryen Talabijin Na Kasar Sin Masu Inganci A Vietnam
- Daidaitaccen Tunanin Sin Shi Ne Dabarar Fuskantar Da “Haukar Amurka”
Kazalika, a cewar hukumar, karin harajin na Amurka ba zai taba yin wata ma’ana ba, zai kuma shiga kundin tarihi a matsayin barkwancin tattalin arziki da ya taba faruwa.
Duba da cewa, ko a yanzu ma bisa harajin da Amurka ta kakaba, kayayyakin Amurka ba za su iya samun karbuwa a kasuwannin kasar Sin ba, idan har Amurka ta kara yawan haraji kan hajojin Sin, bangaren Sin zai yi watsi da hakan.
Sai dai kuma, idan Amurka ta nace wajen neman illata moriyar kasar Sin, Sin din za ta aiwatar da matakan ramuwa, tare da tunkarar wannan yaki har karshensa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp