Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, kasar Sin za ta zurfafa hadin gwiwa tare da bangarori daban daban kan shirin ci gaban duniya, da kuma ci gaba da more damar samun bunkasuwa yayin da Sin take zamanintar da kasa bisa salon kanta.
A ranar 21 ga watan Satumban shekarar 2021, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shirin ci gaban duniya yayin da yake halartar muhawarar babban taron MDD karo na 76. Mao Ning ta yi tsokaci kan wannan batu cewa, a cikin shekaru 3 da suka gabata, an samu karin membobin da suka amince da shirin, da samun nasarori da dama, kana kasashe fiye da 100 da kungiyoyin kasa da kasa da dama ciki har da MDD sun nuna goyon baya ga shirin, da kuma yawan kasashen da suka shiga rukunin abokai na shirin ci gaban duniya ya zarce 80. Kasar Sin ta kafa asusun ci gaban duniya da hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, wanda ya riga ya nuna goyon baya ga ayyuka fiye da 150, kana an fara kafa tsarin cibiyoyin sa kaimi ga bunkasuwar duniya a dukkan fannoni. (Zainab Zhang)