Sinawa na ci gaba da nuna alhini da jimamin rasuwar tsohon shugaban kasar Jiang Zemin, wanda ya rasu ranar Laraba a birnin Shanghai yana da shekaru 96 a duniya.
Da safiyar ranar Alhamis, an sassauto da tutar kasar Sin zuwa rabin sanda a filin Tian’anmen dake tsakiyar birnin Beijing.
Ren Yuhe, wani mazauni birnin Beijing, da ya ziyarci filin Tian’anmen domin martaba marigayin, ya ce lokacin da Jiang Zemin ke jagoranci, an samu ci gaba a fannonin gudanar da sauye-sauye, da bude kofa, da zamanantar da kasar mai mulkin gurguzu.
Jami’an JKS da na sassan hukumomin gwamnatin kasar Sin, da sauran kungiyoyin al’ummar kasar, sun saurari ko kallon sanarwar da aka gabatar ta kafofin talabijin, da radio, da yanar gizo, ga dukkanin jam’iyyar kwaminis ta kasar, da daukacin dakarun sojin kasar, da ma dukkanin al’ummun kasar na kabilu daban daban.
Sun kuma amince cewa, tsakanin karshen shekarun 1980 da farkon shekarun 1990, lokaci ne mai matukar muhimmanci ga makomar jam’iyyar da kasar ta Sin, a lokacin, Jiang Zemin ya jagoranci shugabannin kasar wajen cimma sabon ci gaba na aiwatar da sauye-sauye, da bude kofa a Sin, da ma zamanantar da kasar mai mulkin gurguzu. (Saminu Alhassan)