Gwamna Abdullahi Sule ya cika shekara biyar kan kujerar mulki ko za ka bayyana wa masu karatu irin ci gaban da ya kawowa al’ummar Jihar?
Gwamna Abdullahi Sule tun lokacin da ya fara Takara ya yi nazarin ya karanci matsalolin wannan jihar. Ya kuma gano irin dama da albarkatun kasa da Allah ya ba jihar Nasarawa. Lokacin da ya hau mulki ya yi amfani da wadannan abubuwan inda ya kawo ci gaban
jihar. A shekaru biyar din Allah ya taimakawa Gwamna Abdullahi Sule ya samu nasara kan abubuwan da ya tsara domin amfanin jihar Nasarawa.
Gwamna Abdullahi Sule ya sauya fasalin jihar a bangarori daban- daban.
Misali akwai sabuwar Sakatariyar Gwamnatin jihar wadda yanzu haka aiki ya yi nisa, ana kokarin hada manyan ma’aikatun Gwamnatin jihar wuri guda.
A hanyar Akurba akwai tagwayen hanyoyi da suka taso daga Total zuwa zauren majalisar dokoki ta jihar. Bugu da kari ya sauya fasalin Lafia fadar Gwamnatin jihar da hanyoyi ko wane lungu da sako.
Sai kuma ayyukan abubuwan more rayuwa, haka zalika bangaren kiwon lafiya da bangaren Ilimi domin al’umman jihar sun gani a kasa.
Jihar Nasarawa tana kan gaba cikin jihohin da ke zaman lafiya ko mene ne sirrin samar da wannan zaman lafiya?
Sirrin ba wani sabon abu ba ne saboda Gwamna Abdullahi Sule bai bari har sai abu ya lalace sannan a gyara ba. Tun kafin ya faru ake daukar mataki. Da zarar ya ji kiris yakan tara Jami’an tsaro da Sarakuna da Malaman addini, masu fada aji, da kuma Shugabannin kabilu domin daukar mataki.
Mutum ne mai hangen nesa yana hada kan al’umma da nuna masu mahimmancin zaman lafiya. Ta hakane al’umman jihar Nasarawa suke son juna aka samu dauwamammen zaman lafiya mai dorewa.
Gwamna baya bambanta wata kabila ko addini yana hada kan al’umma kowa ya kawo shawararsa ta yadda za a samu zaman lafiya a jihar. Baya wasa da shawarwarin Jami’an tsaro da yan Sintiri. Ana kuma ba su kayan aiki domin karfafa masu gwiwa ta haka ne al’ummar jihar Nasarawa suke barci da ido biyu.
Jihar Nasarawa tana da dinbin albarkatun kasa, Gwamna Abdullahi Sule tun hawan shi mulki yake fadi tashi domin jan hankalin masu zuba jari dan ganin ‘yan jihar sun ci gajiyar arzikin, ko wace nasara aka samu zuwa yanzu?
An samu ci gaba sosai. Sai dai batun zuba jari ba abu ne da idan ka zuba yau gobe ka kwashe ba. Saboda jama’a na korafi cewa an ce an kawo masu zuba jari har yanzu ba su ga komai ba.
Duk mai zuba jari sai ya yi nazarin yadda zai zuba jarinsa ya yi la’akari da zaman lafiya da kasuwar da zai kai abinda ya samo da ma’aikata masu sarrafa wannan abin.
Gwamna Abdullahi Sule abin da ya fara yi sai da ya tabbatar da duk abubuwan da masu zuba jari za su nema an tanade su, shi ya sa ya kafa hukumar NASIDA dake tafiyar da wannan bangaren. Duk mai zuba jari ba ya tsoron zai yi asara ko kuma a wayi gari a ce an lalata ko an rufe wurin. Akwai ka’idoji da aka shinfida wanda kowa zai bi kafin fara hakar ma’adanai. Wanda ya sanya mai zuba jari ba zai yi fargaba ba.
Akwai kamfanin Dangote da yake da dumbin ma’aikata ‘yan jihar, kuma kamfani ne na sarrafa suga da zai shayar da ‘yan Nijeriya kusan kashi biyu bisa uku. Akwai Agoro Scikin wanda ya kan janyon manoma ake basu iri da maganin kwari da sauransu domin bunkasa harkar Noma.
Allah ya albarkaci Jihar Nasarawa da ma’adinan Lithium wanda yanzu a duniya shi ne take tashe. Ton daya ana sai da shi da tsada. Akwai ‘yan Chana sun Samar da Kamfanin sarrafa shi a jihar Nasarawa.
Gwamna Abdullahi Sule ya canza tsarin hakar Ma’adanai sabanin yadda a baya mutane na hakar Ma’adanai ba tare da Gwamnatin jihar ta sani ba. Su haka idan sun tashi su bar rami, su lalata guri su yi tafiyarsu. Ba tare da Gwamnati ta san me suka diba a jihar ba, duk da cewa Ma’adinan Kasa hakki ne na Gwamnatin Tarayya.
Gwamnatin jihar ta fitar da tsari idan za ka hake ma’adanai in son samu ne ka gina wajen tace ma’adanai a jihar. Saboda a san abin da ka samu, sannan mutanen jihar su samu aiki. Misali, Ma’aikatar Sarrafa Ma’adanai ta Lithium da aka bude kwanan nan a Odege da ke jihar Nasarawa. Ton dubu hudu take sarafawa a duk rana. Yanzu ‘yan jihar Nasarawa mutum dari biyar suka samu aiki a wajen. Kuma wajen gwaje-gwajen ‘yan Nijeriya ake koyar da su yadda ake aiki. Saboda idan sun iya nan gaba su koyar da na baya.
Wannan ya dora Jihar Nasarawa kan tsarin ci gaban tattalin arziki.
Yanzu haka kuma an gano wani wurin da wadannan Ma’adanai na Lithium suke kwance fiye da wancan duk a Nasarawa, kun ga wannan taimakon Allah ne saboda jajircewar Gwamna Abdullahi Sule.
Jihar Nasarawa tana da kasar noma mai albarka, me Gwamna Sule yake yi wa manoma musamman kanana da ke karkara?
Kananan Manoma su ne ‘yan gatan Injiniya Abdullahi Sule. Gwamnati tana sayen taki kan 20,000 ta sayar wa manoma 11,000, ga iri ga maganin kwari yanzu haka ga motocin Noma Gwamnatin ta sayo za a raba wa manoma. Kuma hukumar kula da aikin gona tana taimakawa da shawarwari kan yadda za a samu ci gaba.
Yanzu jihar Nasarawa ita ce kan gaba wajan noman Ridi da Doya da Rogo. Ko a kwanan nan gwamnati ta ba kungiyar kananan manoma milyan arba’in su raba domin bunkasa aikin gona.
Ina maganar Tituna a karkara da sauran kananan hukumomi?
Gwamna Abdullahi Sule ya gina tituna a karkara domin manoma su samu hanya mafi sauki ta kawo amfanin gona zuwa kasuwanni cikin gari.
Ba za mu iya lisafa titunan da Gwamna yayi su a Karkara da Kananan hukumomi ba saboda an yi su ne da tsari da tunani yadda al’ummar guraren za su amfana da mulkin demokurdiyya wuraren da a baya ake daukar awonni ana tafiya yanzu da aka yi titi sai ya koma tafiyar mintuna.
Kula da yin ingantattun ayyuka cikin tsari ya kai jihar Nasarawa zama ta daya a fadin Nijeriya.
A sauran jihohi ma’aikatan Gwamnati suna kokawa dangane da batun albashi ya abin yake a Jihar Nasarawa?
Mu ko Jihar Nasarawa Allah ya kawo mana saukin wannan matsalar, a gwamnatin baya an yi kuka amma yanzu ma’aikatan gwamnati suna morewa a Jihar Nasarawa.
Wannan tsari ne na Gwamna Abdullahi Sule da yake cewa ka bai wa ma’aikaci hakkinsa tun kafin zufar jikinsa ta bushe. Saboda a lokacin da ya yi aiki bai samu matsalar biyan albashi ba. Dan haka bai ga dalilin danne hakkin mutumin da ya yi aiki ba, bare a kasa biyansa a kan lokaci.
A Gwamnatin baya ma’aikatan sun fuskanci matsalar biyan albashi inda ta kai a wata ana basu ko rabi da rabi ko abinda ya samu. Tun zuwan Gwamna Abdullahi Sule ma’aikatan Gwamnati na samun albashi cikakke kuma akan lokaci.
Baya ga haka a lokacin Gwamna Abdullahi Sule Ma’aikatan Gwamnatin jihar Nasarawa sun samu karin girma. Sannan an dauki sabbin ma’aikata da yawa. Sannan ana tura su taron wayar da kai da sanin makamar aiki wanda a baya ba a yin hakan.
Abin burgewa shi ne yadda Gwamna Abdullahi Sule ya magance matsalar ‘yan Fansho, kai akwai wadanda tun ana jihar Filato wasu ba su samu hakkinsu ba.
Gwamna Abdullahi Sule ya samar da tsari duk wata uku ake ware miliyoyi ana biyan su, daga bayan nan ma har ta kai biliyon aka ware ana biyan su. Masu bin bashin garatuti an sallame su, masu fansho suna samu a kai a kai. Yanzu haka babu mai cewa a bangaren jihar yana bin bashi ko na wata daya. Sai dai idan da wata matsala ce daban.
Idan ka ga matsala ta fansho to sai dai ko daga kananan hukumomi, kuma wani lokacin jihar tana sa hannu domin ganin an magance matsalar.
Daga karshe mene ne kiranka ga al’umman Jihar Nasarawa?
Kamar yadda Gwamna Abdullahi Sule yake cewa shugabanci ba na mutum daya ba ne, duk mai kaunar jihar ya kasance ya ba da tashi gudumawar.
Ta yaya za ka bada gudunmawa? A wajen aiki ne ko a kasuwa ko gona ka yi aikinka tsakani da Allah. Kowa na da rawar da zai taka.
Akwai makarantar koyon sana’a mai bangarori goma sha hudu, mai suna Kwamanda Abdullahi Ibrahim mutum ko da ya gama Digiri idan bai samu aiki ba, zai iya zuwa can ya koyi sana’ar da yake so idan ya gama akwai jari da gwamnati ke badawa domin mutum ya bunkasa sana’arsa da ya koya. Wadanda ake yayewa a makarantar ana ba su jari.