A ci gaba da kawo muku tsokaci game da bunciken masana kan sirrikan Mata wanda mafi yawan Maza ba su san su ba, masanan sun bayyana cewa; Mace tana da saurin tausayawa da taimakawa, sannan tana da saurin Gorantawa. Haka kuma Mace takan rike sirri ne idan ta san tona asirin abun zai shafeta. Muddin ta san sirrin da aka ba ta ba wanda zai zubar mata da mutunci bane, cikin sauki za ta fada wa wasu ta ce musu ita sirri ne aka ba ta suma ta basu sirri.
Mata tamkar gishiri suke, idan suna waje ba lallai bane a fahimci hakan. Amma idan har babu su a waje kowa sai ya fahimci babu su. Sai dai a tawa fahimtar ba dukka Mata ne suke a hakan ba, dan ba dukka ne aka taru aka zama daya ba, kamar yadda suma mazan ba dukka ne suka taru suka zama dayan ba. Akwai Mata masu saurin gorantawa akwai kuma matan da ba su da saurin gorantawa ba ma sa yi kafin su yi sai an kai su bango, amma hakan ba wai yana nufin babu su, ko kuma masu gorantawar ba su da yawa ba, a’a! Mafi yawan rinjayen masu gorantawa ne, domin mafi akasarin Mata sukan gorantawa mutum ta kowanne fanni, ba wai lallai iya zamantakewa irin ta auratayya tsakanin miji da mata ba, ta ko ina mace na iya gorantawa mutum ko da kuwa ba a taba haduwa da juna ba (haduwar ‘Social Media’).
Sabanin maza da mafi yawansu ba su san gorin ba, idan na ce ba su sani ba, ina nufin basu cika yinsa ba domin su din ma ana samun masu yi, akwai Mazan da duke da gori har akan hakkin daya rataya kansu, gashi dai hakkinsu ne da ya rataya a wuyansu wanda za su sauke wa iyalinsu amma watarana sai sun goranta wa iyalin duk yawan abin da suka yi musu da sauran abubuwa. Hankalin ne dai na namiji ya fi na mace, masu gorantawar ba su da yawa cikin Maza kamar yadda suke da yawa cikin mata.
Mafi rinjayen wasu Matan duk abin da za su yi wa mutum na alkhairi akasarinsa suna yi suna lissafawa ne ba dan komai ba sai dan su tara shi ya yi yawa har zuwa lokacin gorantawa, wanda a lokacin ne za a rinka lissafo wa ana goranta wa wanda aka yi wa, walau miji ko kawa ko zamantakewar unguwa ta makobtaka ko ‘Yan uwantaka ko hadakar aiki, ta ko ina ana samu kuma ana iya gorantawa. Dan akwai mutanen da har alla-alla suke abin taimakawa ya yi su taimaka ko da jikinsu ko da aljihunsu dan kawai a shigar da shi sahun lissafin da za a goranta watarana. Kun ga wannan kenan ya zama ba dan Allah ba, ba da zuciya daya ba, Allah ya sa mu dace, amin. Tabbas! haka ne, Mata na da tausayawa sosai dan mace na iya daukar damuwar da ba ta ta ba ta dora wa kanta musamman akan mijinta.
Sai kuma batun rike sirri wanda aka ce mata basa iya rike shi sai idan sun san tona sirrin zai shafe su, a tawa fahimtar shi din ma kamar bayanina na baya ne, ba dukka aka taru aka zama daya ba, kuma su mutane daman ai akwai na gari akwai akasin hakan a ko ina, kuma halayyar kowa ta bambanta ba za a ce Mata haka suke ba gaba daya, sam! ba haka suke ba, akwai mata masu rike sirri sosai, sai dai ba su da yawa a yanzu.
Mafi rinjaye a wannan zamanin na marasa iya rike sirri ne domin zamanin ya sauya ba kamar zamanin baya ba, mafi yawan Mata da mazan duk kusan hakan ne amma Mata sun fi yawa, da son jin zancen da ba a yi niyyar sanar da su ba, a ji a je a isar a wajen da ya dace da wanda bai dace ba, dan wasu ko da baka fada musu sirrinka ba toh su da kansu za su rinka bugar cikinka da wasu magan-ganun dan kawai ka fayyace musu sirrin kanka a dabarance, wasu kuma sukan jira da zarar wani abun bakin ciki ya same ka wanda bana farin ciki ba kokari za su yi su yi ta nemanka a ranar zama za ka yi tamkar wani ‘Celebrity’ dan tsananin kira da neman da jama’a suke wa mutum walau kawaye ko ‘Yan unguwa da sauransu. Amma da zarar abun farin ciki ya sameka sai ka ji shuru tamkar mara masoya me cutar bakin jini, wani sa’in ma hatta kawarka ba za ta kira ta tayaka wannan farin cikin ba, balle kuma a zauna a yarda da mutum dari bisa dari ka warware masa damuwarka da zummar ya baka shawara ko ka furta zuciyarka ta yi sanyi.
A yanzu kamata ya yi mutane su farka daga baccin da suke yi, su koyi boye sirrikansu iya zukatansu domin kuwa muddin za su fito su furta shi su ce sirri ne toh kuwa sai an bayyana shi har a inda ba sa tsammani, kar mutum ya yi tsammanin ya bayyana abin da ke damunsa a rai ya fada wa wani ya saki baki yana bacci har da munshari da sunan ya fidda abin da yake zuciyarsa ya ji sanyi, babu jin sanyi muddin ka furta toh kuwa ka fada wa duniya ne halin da kake ciki. A yanzu mafi yawan masu wayo wanda suka san yadda wayo yake da dabara sukan tace magana ne ya yin furtata musamman in suna son isar da sako ya isa cikin sauki ga wanda su ke son a isar wa, hanya daya kawai suke bi su samu wata su sanarwa zancen su ce sirri ne, toh ko awa guda ba zai ba zancen zai fara yawo yana zagawa gurare daban-daban, daga nan har ya isa kunnen wanda ake so ya isa.
Wannan a takaice kenan yanzu kuma zan je ga ra’ayoyin mabiya wannan shafi domin jin na su ra’ayin dangane da wannan batu, ga su kamar haka:
Zara’u Abubakar (Dr.Zarah) Brigade Gama-D Karamar Hukumar Nassarawa:
Eh! Gaskiya haka ne mace na da saurin tausayawa sosai nan da nan tausayi ya kamata, amma kuma nan take abin da bai kai ya kawo ba yanzu sai ta goranta maka akan sa. Gaskiya ba kowace mace ba ce a hakan gaskiya sai me karamin tunani ko kuma in ce wacce ba ta san me ake ma nufi da sirri din ba. Eh! toh, gaskiya haka ne kamar misalin ta fadin rayuwa a cikin gida duk inda babu mace ai dole a gane cen kura cen yana da dai sauran su saboda gaskiya duk irin gyaran da Namiji zai tsaya ya yi wa gida ba kamar mace ba wallahi, domin dama cen da macen ya dace don haka ko ya ta dan matsa ba ta nan dole a ga bambanci musanman idan me yi ce akai-akai.
Hauwa Salisu (Haupha) Jihar Katsina:
Tabbas! Mace na da mugun tausayi na gasken-gaske wanda da wahala a samu namijin da ke da shi sai da wani dalili. Sai dai gorin mace ba ko’ina take yinsa ba sai an zo madakata wato tsakaninta da mijinta idan zai kara aure to ai gori har wanda ya manta sai ta tuna ta yi ma shi. Tabbas! na yarda da hakan, mace ba ta taba yarda ta tona sirrin da zai zubar mata da mutunci amma fa ba wani lamarin mamaki ba ne don ta tona ta ja kunnen wanda ta gaya wa ba. Sosai kuwa domin duk lalacewar mace a cikin gida idan ta gusa sai an ga ranarta watarana, haka kuma sai an ce “Yau ga ranar wance’. Ko ace “Da wance na nan da ba haka ba” da sauransu, ai ko kare na da rana balle mace.
Bilkisu Musa Galadanchi Sokoto, Nijeriya:
Babu shakka mace tana da saurin tausayawa fiye da tunani, saboda ai mace uwa ce. Maganar gorantawa kuma ba zan musa ba, saboda mata suna da rauni fiye da kima tunanin su ba kamar na namiji ne ba. Wannan maganar ba gaskiya ba ne, labari ne kawai irin na kanzon kurege, kamar yadda a mazan ma halayya kowa daban haka a matan ma akwai nagartattu masu amana da rike sirri. Sannan sukan rike sirri ko dai ba zai amfanesu da komai ba. Babu shakka wannan maganar haka take, duk inda mata suke tabbas ‘yar manuniya za ta nuna hakan, inda duk babu mata kuwa za ku fahimci hakan da kanku, bahaushe ya ce rikon gida sai mata.
Fadila Lamido daga Jihar Kaduna:
Tabbas! Mace na da tausayi, da zarar za ka fada mata matsala za ta iya shiga cikin matsalar tsundum, har ma ta ji tamkar ita ce abun ke faruwa da ita. Kuma duk yadda za ta yi ta ga ta kawo mafita akan yadda za ta taimaka za ta yi, maganar gori kuma ai duk dan halak ba ya manta halacci, idan har wadda aka tausaya wa zai zama kaza ci ki goge baki mace tana iya goranta wa, san da za ta goranta ma ba ta sane ba, saboda mu mata rauni ne da mu, idan har mutum bai manta ka taba yi masa hallaci ba ko me zai kawo gori?, Wadda baya manta baya ko wani abun ka yi masa na bacin rai idan ya tuna ka taba tausaya masa sai ya yi kokarin ganin ya kawar da bacin ran saboda bai mance alheri ba, idan har mutumin da aka tausaya wa ya zama me mance baya kadan ne daga cikin mata kan iya jurewa ba tare da sun goranta ba. Ba gaskiya bane ace wai mace tana rike sirri ne idan ta san tona asirin abun zai shafeta, sam! ba haka bane, mace na rike sirri ko da ace ba ta da alaka da fasuwar abun, duk wadda ya kwashi sirrin sa ya fada maka ya yadda da kai ne, ya gama baka amana, kuskuren da wasu ke yi basa tsayawa su yi dogon nazarin mutumin da zabsu bawa sirri, ya dace ace kafin ka ba da sirri ka karanci halayen mutum, ka tabbatar da cewa yana daraja amana kafin ka fada masa sirrin ka, amman duk mace da za a fada mata sirri ta fada wa wasu ta ce musu ita ma Sirri ne aka bata ni ma bari na baku Sirri a nawa hangen wannan ba ta ma san me take ba, anan gurin sai dai ace ya koma nau’i na munafunci.
Hafsat Moh’d Arabi Jihar Kaduna:
Bari na fara da ‘Gori’ da an ji wannan suna a halkance za a tabbatar ba abu ne me kyau ko dadi ba wanda shiyasa ba shi da dadin fade ko akan harshe. Gori Mummunar dabi’a ce wacce duk Mace ta gari ko Namiji na gari ba zai so hada hanya da shi ba saboda rashin dadinsa ko yi maka aka yi ya kake ji balle ace kai ka iya budar baki kai wa wani shi ko kika iya bude baki kiwa Mijinki Gori haba ‘yar uwa. Manzon Allah (S.A.W) ya ce “Duk matar da ta goranta wa mijinta a bisa dukiyarta, ta ce ai daga dukiyata kake ci, to da za ta yi sadaka fisabilillahi da dukiyar Allah ba zai karba mata ba, har sai mijinta ya yarda da ita”, to kin ji fa ‘yar uwa. Sai dai ana samun irin matan nan wanda ko ashana suka siya sai kaji suna shekaran jiya ma ai ni na siyi ashana da kudi na ko ka ji ana ai ranar ma ni na yi cefane kuma ba biyana zai yi ba ko ace kuma ba ka biya gasu nan kala-kala dai. Shawarata ga Masu wannan halin lallai mu guji wannan mummunar dabi’ar ga mazajenmu, mataye, abokai, kawaye dan sam! babu kyau ba dadi. In ka/kin ce kina dashi ai bake kika yi ba kanki/ka inbaki/ka manta ba. Wanda ya baki na iya karbewa ko yaushe ya ba wanda bai da shi ko kuma ya kara miki in kin kasance ta gari. In mun yi Alkairi Mata dan Allah ya zama tsakani da Allah ne a daina zuwa ana na ba ta kaza ko na mata kaza ko ni nayii cefane da sauransu Allah yasa mu dace Ameen. Rashin Sirri ba bakon abu bane a wannan lokacin haka cin amana. Allah ya kawo mu wani zamani ne yanzu wanda samun aminin kwarai ke matukar wahala, za ki ga mutum kina zaune zai shiga rayuwarki ya nuna shi masoyinki ne na kwarai, Wani ma za ki iya cewa ba ki da wani masoyi da ya kaishi a duniya anma kash! Da an yi nisa sai ki tarar ba mai kwance miki kunshin zani a kasuwa irinsa. Wani dama can tun farko burinsa ya shige ki ne dan ya rusa ki ko wata mummunar manufar a karshe ya ci amanarki. Wasu kuma kana amintaka da su suna da wasu aminan a gefe da kin ce za ta kai wa waccan wanda aka yi rashin sa’a kan Kisan meke faruwa komai ya ruguje an kai inda baki tunani. A zamanin ‘da’ in mu kai duba akwai aminai na amana sosai wanda za ki ga ya bi har ‘ya’ya da jikoki ana zumunci an zama daya a kashe a binne tare anma a wannan zamanin an samu akasin wannan zaman takewar wanda a ganina Hassada da kyashi suna daga cikin manyan abubuwan da ke jawo mana wadannan matsalolin wanda muddin ba mu gyara zuciyoyinmu ba dole abubuwa haka su ci gaba da tafiya. Mutumin da burinsa da ya samu na kusa da shi su samu. Kai! Wani zai iya hakura ma dana shi wasu su samu amma a wannan zamanin ana tare da kai da abun samu ya zo maka sai bakin ciki da Hassada da kyashi ya shiga ya bata komai ba tare da laifin gyara ko dalili ba. Ko In ce akwai dalili wanda shi ne ka ci gaba wanda so ake a ci gaba da ganinka babun. Wasu in abun bakin ciki ya sameka har murna suke maimakon a tayaka bakin ciki. A karshe zan ce Sirri abu ne me kyau matuka haka ana samun marasa sirrin sam! sai dai a wannan zamanin ‘mostly’ wasu yarda ke kaisu ga ‘sharing’ matsalolinsu dan akwai wasu abu a rayuwar mutum wanda in ya dameshi in ba ya tattauna abun ba sai ya iya haifar masa da wata matsalar. To kun ga matsalar babba shi ne rashin aminan kwarai da muke fama da su a wannan zamanin kawar kawa, abokin aboki, duk abun daya ne Allah dai ya sada mu da masoya na gari ya kuma sake shirya mana Zuciyarmu baki daya ya yaye mana matsaloli Ameen.