Tun bayan barkewar annobar COVID-19, Amurka ta share fagen kirkiro karairayi, da labarai marasa maana, masu nuna yatsa ga kasar Sin, inda ta yi ta zargin Sin da laifin boye bayanai, ko kasancewa asalin bazuwar cutar. Irin wadannan labarai marasa tushe da yan siyasar Amurka suka rika bazawa, sun karkatar da tunanin Amurkawa, kuma burin yan siyasar shi ne kare gazawar su a fannin yaki da cutar a cikin gida yadda ya kamata.
Masharhanta da dama sun rika bayyana cewa, yan siyasar Amurka na kirkiro karin zarge-zarge, da siyasantar da batun wannan cuta, a matsayin wata dabara ta kawar da tunanin Amurkawa daga tarin matsalolin da ke addabar kasarsu, kama daga hauhawar farashi, da karyewar jarin bankuna, da koma bayan tattalin arziki da sauran su.
A baya bayan nan, alkaluman kafofin watsa labarai na Amurka sun nuna cewa, Amurkawa da dama sun yarda cewa, annobar COVID-19 ta samo asali ne daga dakin gwajin kwayoyin cuta, sabanin bullar cutar daga yanayi na asali. Wadannan alkaluma dai sun yi daidai da raayin gwamnatin kasar, duk da cewa ba wasu shaidu na kimiyya da suka tabbatar da hakan.
Duk da cewa abu ne mai muhimmancin gaske a bi matakai da suka dace na gano asalin annobar COVID-19, domin yin kandagarkin aukuwar irin wannan annoba a gaba, ya dace a bi dabaru na kimiyya, da kwarewa domin tabbatar da hakan.
A watan Faburairun bara, hukumar kiwon lafiya ta MDD WHO, ta fitar da rahoton hadin gwiwa tare da kasar Sin game da asalin wannan cuta, bayan binciken makwanni 4 da aka gudanar a Sin, inda sakamakon ya tabbatar da cewa, zai yi matukar wuya, a ce wannan cuta ta bullo ne ta wani dakin gwajin kwayoyin cuta.
A baya bayan nan, mun ga yadda Amurka ta sake dauko batun gano asalin wannan cuta, ta hanyar kaddamar da wani kudurin hukuma na gudanar da bincike, bisa dogaro da siyasa maimakon kimiyya. Ga alama dai yan siyasar Amurka suna son bin raayin kashin kai. Suna gamsuwa da kila-wa-kala, ko hasashe wajen tabbatar da zaton su, wanda hakan ya sabawa kwarewa, da shaidu da masana kimiyya ke amfani da su wajen tabbatar da asalin duk wata.
Illar wannan mataki shi ne karkatar da tunanin alumma daga gaskiya. Da amfani da siyasa a matsayin makamin cimma burin kashin kai, da haifar da rudani tsakanin alumma.
Gano asalin duk wata cuta na daukar lokaci mai yawa, kuma ya kamata yan siyasa su daina bata lokaci wajen furta kalamai marasa dalili, ko shaidun kimiyya. Kaza lika matakin yan siyasar Amurka na kin yin hadin gwiwa da masana kimiyya a wannan aiki, ba zai haifar da komai ba, illa kara muzanta kasarsu a idanun duniya.