Ya hada zoben aure ta hanyar amfani da gwangwani kuma ya nemi na aure shi. Tabbas na amince,” a cewar Baleria Subotina.
“Masoyina ne na kwarai. Zobinanmu sun yi kyau sosai,” in ji ta.
- Ba Gwamnati Ce Kadai Za Ta Magance Yawan Barace-Barace Ba
- Kabilar Bayankole Da Innar Amarya Ke Jima’i Da Ango Domin Gwaji
Ita da saurayinta Andriy Subotin mai shekara 34 kuma sajan a rundunar sojin Ukraine, suna shirin daura aure a Mariupol kafin yaki ya barke tsakanin kasar da Rasha.
Sun yi ta burin hada gagarumin biki tare da ‘yan’uwa da abokan arziki.
Sai dai jim kadan bayan mamayen da Rasha, dakarun kasar sun wuce kai-tsaye zuwa wannan gari mai tashar jiragen ruwa kuma mai muhimmanci a Kudancin Ukraine kuma suka yi masa zobe cikin ‘yan kwanaki.
Dakarun Rasha sun yi ta luguden wuta a kan Birnin Mariupol, tituna suka dinga ci da wuta, babu abinci, babu wuta, babu ruwa, babu wata hanyar barin garin.
Garin ya shafe kusan wata uku a garkame. An yi imanin cewa an kashe dubun dubatar fararen hula.
A gefe guda kuma, mazauna Mariupol da yawa sun nemi mafaka a ginin masana’antar karafa ta Azobstal, inda ake da maboya sama da 30 wadanda aka gina tun lokacin Tarayyar Sobiet saboda tsoron harin nukiliya.
A nan ne kuma aka daura wa Baleria aure – kuma ta zama bazawara a kwana biyu kacal.
‘Yunwa a kan iyaka’
Baleria mawakiya ce lokacin da Rasha ta afka wa Ukraine. Daga nan kuma sai ta zama kakakin Bataliyar Azob.
Yayin da Rasha ke tsananta hare-hare a kan Mariupol, dole aka tilasta wa dakarun Ukraine guduwa zuwa maboyar Azobstal tare da fararen hula.
Mashigar maboyar kamar rami take, kuma sai mutum ya yi ta yin kasa a kan matattakalar da suka lalace, in ji Baleria.
Mutane sun giggina madafa a cikin maboyar, inda ake sake girka abincin da aka ci aka rage.
Idan suka samu fulawa sai su kwaba ta don hada ket (cake).
“Muna kiran sa burodi amma dai ket ne kawai da ruwa. A haka muka rayu. Yunwa ce kawai a wurin,” a cewar Baleria.
“Mun zama kamar wasu beraye saboda duk abin da muka samu ci kawai muke. Mu kan yi barci a kasa ko kuma a kan tsimma.
“A wani wurin babu haske ko kadan, amma sai da idanuwanmu suka saba har ma ya zama jiki. Amma maganar gaskiya rayuwarmu ta daban ce a lokacin.”
A ranar 15 ga watan Afrilun 2022, an jefa wani babban bam a kan masana’antar, wanda ya raunata baleria.
“A cikin gawarwaki aka gano ni, kuma ni kadai ce a raye. Sa’a ce kawai, amma kuma bala’i ne me tsauri.”
Bayan rauni da ta ji a ka saboda buguwa, Baleria ta shafe kwana takwas a asibitin da ke maboyar ta karkashin kasa tare da sauran marasa lafiya.
“Ba su iya samun kulawar da ta dace ba saboda babu isassun magunguna. Warin jini da kuma na rubewar abubuwa sun cika wurin,” in ji ta.
Shi ma mijin Baleria mai suna Andriy a Azobstal yake. Jim kadan bayan raunukan da ta ji, nan take ya nemi aurenta kuma a wurin.
A ranar 5 ga watan Mayu, ma’auratan suka sanya hannu kan yarjejeniyar aure kuma suka aika wa iyayen Andriy kwafin takardun ta intanet a Kyib, wadanda daga baya suka je ofishin hukuma don karkare shirin.
Sun yi bikinsu a maboyar sanye da kakin soja a matsayin kwalliyar biki, da kuma zobinansu da aka yi da gwangwani.
Andriy ya yi alkawarin zai saya mata zoben gaske idan aka gama yakin.
Amma an kashe shi ranar 7 ga watan Mayu a bakin daga.