Sojoji da hadin gwiwar ‘yansanda a ranar Alhamis 2 ga watan Nuwamba, 2023, sun ceto wasu mutum biyu da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a unguwar Yargoje da ke karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.
An yi garkuwa da masu yi wa kasa hidimar ne a lokacin da suke kan hanyarsu daga Edo zuwa jihar Katsina.
Sanarwar da Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya ce jajircewar da jami’an tsaro suka yi ce ta sa aka kwato wadanda abun ya shafa.
Ya ce, “Aikin gaggawa ta hanyar hadin gwiwar sojojin Birgediya 17 da ‘yansandan Nijeriya suka yi ya sa aka samu nasarar ceto wadanda lamarin ya shafa daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.”
Janar Nwachukwu ya ce an bai wa masu yi kasa hidimar kulawar da ta dace.
Don haka ya nemi hadin kan jama’a wajen samar da bayanan da suka dace don inganta ayyukan da sojoji ke yi na tunkarar wasu miyagun laifuka da ke barazana ga tsaro a jihar.