Dakarun Operation Hadarin Daji a Jihar Zamfara sun dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai garin Anka hedikwatar karamar hukumar Anka tare da kashe wani dan bindiga daya a ranar Litinin.
Leadership Hausa ta tattaro cewa sojojin da suka yi aiki da rahoton leken asiri game da ‘yan ta’addan sun yi yunkurin kai hari a garin, inda suka yi artabu da ‘yan bindigar da ya dauki tsawon sa’o’i da dama.
Majiyoyi sun shaida wa Leadership Hausa cewa sojojin sun gudanar da sintiri a kauyen Tungar Mai-Rakuma da ke karamar hukumar Anka kuma an yi artabu da su.
Sai dai sojojin sun yi galaba a kan ‘yan bindigar inda suka kashe dan bindiga guda daya sannan kuma suka samu nasarar kwato babur daya kirar AK-47 da alburusai.
“Bayan arangamar, an kashe ‘yan bindiga guda daya, sannan an kwato kayayyakin sun hada da AK-47 guda daya, babur guda da harsasai,” in ji wata majiyar soja.
Sojojin sun ci gaba da mamaye yankin gaba daya domin kama ‘yan bindigar da suka tsere.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp