Rundunar sojin Nijeriya a Jihar Zamfara, sun yi nasarar hallaka kasurgumin dan bindiga da ya addabi jihar, Junaidu Fasagora wasu jiga-jigan yaransa.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, rundunar ta ce ta yi nasarar kashe Fasagora tare da yaransa da dama ne bayan wata arangama da suka yi a Karamar Hukumar Tsafe.
- Sojoji Sun Wanke Fursunoni 200 Da Ake Zargin Alaka Da Boko Haram A Borno
- Ummita: Kotu Ta Yanke Wa Dan China Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya
“Junaidu Fasagora da kungiyarsa ta ta’addanci sun dade suna addabar mutane da satar mutane da sauran ayyukan ta’addanci a jihohi da dama a Arewa maso Yamma,” in ji rundunar.
Ta kara da cewa kawar da su din wata muhimmiyar nasara ce a yakin da ta ke yi da ta’addanci.
Wannan nasara tana zuwa ne sa’o’i kadan bayan da rundunar sojin ta ce ta kawar da wani dan bindiga da kwato makamai a Karamar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.
Wannan dai na zuwa ne bayan wata ganawa da Gwamna Dauda Lawal ya yi da Shugaba Tinubu a kan matsalar tsaro da ta addabi jihar.
Fasagora da yaransa sun yi kaurin suna wajen sace mutane da neman kudin fansa a Jihar Zamfara.