Wata babbar kotu a Jihar Kano, ta yanke wa dan China da ya kashe Ummukulthum Buhari da aka fi sani da Ummita, Mista Geng Quanrong, hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji na babbar kotu a Jihar Kano da ke zamanta a Miller road a Bompai ne, ya yanke wa Quandong hukuncin bayan samunsa da laifi.
- Dalibai 137 Aka Sace A Kuriga Ba 287 Ba – Uba Sani
- HOTUNA: Yadda Jami’an Tsaro Suka Lalata Haramtacciyar Matatar Danyen Mai A Ribas
A watan Satumban 2022 ne, Geng ya shiga gidansu Ummita ya kashe ta har lahira.
Bayan ya kashe ta ya tsere amma daga bisani ‘yansanda sun kama shi kuma suka gurfanar da shi a gaban kuliya.
A lokacin da ake yi masa tambayoyi a kotu, ya ce Ummita ta yaudare shi tare da auren wani bayan ta yi masa alkawarin za ta aure shi.
Geng ya kara da cewa, a lokacin da suka fara shirye-shiryen aurensu, ya saya mata kayan aure na Naira miliyan 1.5, sannan ya saya wa kawayenta kayan 700,000.
Ya ce duk da ta yi aure amma ta ci gaba da neman kudi a wajensa.
Ya ce, “Baya ga makudan kudaden da na kashe mata, na kai ta wurare kamar Bristol Palace da Central Hotel don ta ci abinci.”
Ya kara da cewa ya saya mata kayan ado na gwal da kudinsu ya kai Naira miliyan biyar, sannan ya kashe mata sama da Naira miliyan shida lokacin da ta karatu a Jami’ar Usman Danfodio da ke Sakkwato.
A ranar Talata ne alkalin ya yanke wa Geng hukuncin kisa ta hanyar rataya.