Sojojin da ke aikin atisayen Whirl Stroke (OPWS) sun kama wasu mutane huɗu da ake zargin da ta’addanci tare da ƙwato wasu makamai a ƙauyen Tau da ke ƙaramar hukumar Ardo-Kola a jihar Taraba.
Mai magana da yawun runduna ta 6, Kyaftin Olubodunde Oni, ya bayyana cewa aikin ya biyo bayan wani kiran gaggawa game da shigar wasu mutane ɗauke da makamai yankin Tau. Sojojin sun mayar da martani da sauri, inda suka kama mutanen hudu, uku daga cikinsu suna da bindigogi.
- An Kammala Horon Hadin Gwiwa Tsakanin Sojojin Saman Sin Da Masar Cikin Nasara
- Tawagar Hafsoshin Sojojin Afirka Ta Ziyarci Kasar Sin
An kwato wasu kayayyaki daga waɗanda ake zargin, ciki har da bindigogi biyu, da bindiga ɗaya da aka yi a gida, da wuƙaƙe uku, da harsashi 42, da wayoyin hannu huɗu da katin shaidar ƙasa guda ɗaya. Binciken ya nuna cewa wani mai suna Alhaji Ardo Sani ne ya gayyace su, kuma ana binciken rawar da ya taka.
Janar Kingsley Chidiebere Uwa, kwamandan runduna ta 6, ya yaba wa Sojojin saboda gaggawar ɗaukar mataki da kuma ƙwarewar da suka nuna. Ya kuma jaddada aniyar hukumar na tabbatar da tsaron jihar Taraba.
An kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da bayanai masu aminci don taimakawa wajen inganta tsaro a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp