Sojojin Runduna ta 3 tare da haɗin guiwar JTF Operation Enduring Peace, sun kama wani ɗan ta’adda ɗauke da bindigar AK-47, da harsasai 11 a ƙauyen Kaskra da ke Ropp, Karamar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Manjo Samson Zhakom, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce sojojin sun samu kiran gaggawa cewa wasu ’yan ta’adda na shirin kai wa al’ummar yankin Fann a Barkin Ladi, hari.
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Jimamin Rasuwar Mutane A Nutsewar Jirgin Ruwa A Borgu, Ta Umurci NEMA Ta Kai Agaji
- ‘Yan Nijeriya Suna Shan Wahala A Lokacin Da Gwamnatin Tinubu Ta Fi Damuwa Da Aljihunta – Sule Lamido
Ya bayyana cewa bincike ya nuna cewa wanda aka kama ya shirya kai wa ƙauyukan da ke kusa da Nding hari.
Yanzu haka yana hannun jami’an tsaro inda ake yi masa tambayoyi domin samun ƙarin bayani.
Zhakom ya ƙara da cewa sojojin na ci gaba da aikin neman sauran ’yan ta’addan da suka gudu tare da ƙoƙarin ƙwato makaman da ke hannunsu.
Sanarwar ta tabbatar wa jama’a cewa sojoji sun ƙudiri aniyar kawo ƙarshen kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, tare da tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp