Dakarun rundunar Sojijin Nijeriya sun cafke mutune 69 da ake zargi da hannu a fasa-kaurin mai tare da kwace sama da lita 32,000 na danyen kayayyakin man fetur da aka sace a yayin wani sumame da aka gudanar a sassa daban-daban na Neja-Delta.
A cikin sanarwar da Lt. Colonel Danjuma Jonah Danjuma, mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na 6 Division ya fitar a Fatakwal ranar Lahadi, ya ce aikin ya gudana ne tsakanin 11 zuwa 24 ga Agusta, 2025, tare da haɗin gwuiwar sauran jami’an tsaro, inda aka lalata gudanar da haramtattun wuraren tace mai tara (9).
- Fetur Da Ake Amfani Da Shi Kullum A Nijeriya Ya Ragu Zuwa Lita Miliyan 44.3 –NMDPRA
- CMG Ya Yi Bikin Cudanyar Al’adu Mai Taken “Sautin Zaman Lafiya” A Hadaddiyar Daular Larabawa Da Koriya Ta Kudu
A jihar Delta, an cafke manyan motoci guda biyu dauke da sama da lita 15,000 na man da aka tace ba bisa ka’ida ba a karamar hukumar Sapele, inda aka kama mutum uku da ake zargi da hannu. Haka kuma, a Warri North LGA an gano jarka da ganguna cike da danyen mai da aka tace ba bisa ka’ida ba. A Rivers kuwa, Sojoji sun lalata haramtattun wuraren tace mai guda uku, tare da kwace sama da lita 7,000 da kuma kwace jirgin kwale-kwale guda biyu a Degema da Omoku. Haka kuma, a Oyigbo da Okrika an gano sama da lita 3,000 na danyen mai a wuraren da aka kafa wajen tacewa, inda aka kwace ganga, da tukunyar dumamawa da wasu kayan aiki, tare da kama mutum uku da ake zargi.
A Bayelsa kuwa, an gano wurin tace mai ba bisa ka’ida ba a Biseni, da Yenagoa LGA, da inda aka gano tankoki biyu dauke da fiye da lita 7,000 na man da aka sace. A jihar Akwa Ibom kuwa, dakarun Soji sun gudanar da gagarumar sintiri, wanda hakan ya hana masu laifi damar gudanar da ayyukan su.
Sanarwar ta ce duk mutanen da aka kama an mika su ga hukumomin tsaro domin gurfanar da su a kotu, yayin da kayayyakin da aka kwace aka sarrafa su bisa tsarin aikin dakarun.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp