Dakarun Sojin Nijeriya da ke aiki a Wukari, a Jihar Taraba, sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da dillancin makamai.
Mutanen da aka kama su ne Buba Idi mai shekaru 55 da Isiyaka Yusufa mai shekaru 29.
- Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (2)
- Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Alaƙanta Shettima Da Kwatanta Jonathan Da Tinubu Kan Batun Tsige Gwamna
An kama su ne a ƙauyen Byepi da ke kan hanyar Tsukundi, a Ƙaramar Hukumar Wukari, bayan samun sahihan bayanai game da ayyukansu.
Kwamandan rundunar, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya bayyana cewa sojojin sun yi aiki cikin gaggawa da ƙwarewa.
Ya ce wannan samamen na daga cikin ƙoƙarin da rundunar ke yi don daƙile yaɗuwar makamai da kuma tsaurara tsaro a Jihar Taraba.
A yayin bincike, waɗanda ake zargin sun taimaka wajen gano bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya da wata bindiga mai harsashi 16, wayar salula ƙirar Tecno guda ɗaya, da babur ƙirar Bajaj guda ɗaya.
Kwamandan ya ƙara da cewa suna ci gaba da binciken su, kuma ya tabbatar da cewa rundunar ba za ta bar masu laifi su samu wurin fakewa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp