Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta ce dakarunta da ke tsaron cikin gida musamman dazukan cikin Nijeriya sun ceto waɗanda aka yi garkuwa da su 318, sun kuma kama ‘yan ta’adda 74, da ɓarayin mai da sauran masu laifi a cikin watan Nuwamba.
Daraktan Ayyukan Watsa Labarai na Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, ya ce ‘yan ta’adda 69 da iyalansu sun miƙa wuya ga sojoji a Arewa maso Gabas duk a cikin wannan watan.
- Ma’aikatan Shari’a Sun Fara Yajin Aiki Kan Bashin Albashi Da Kuɗin Hutu A Kogi
- Ko Kwalliya Za Ta Biya Kuɗin Sabulu Kan Sauye-sauyen Tinubu Na Inganta Tsaro A Nijeriya?
Ya ce sojojin a yaƙin da suke yi da satar mai sun kama waɗanda ake zargi su 25 da sauran masu laifi, sun lalata wuraren tace mai ba bisa ƙa’ida ba 16, sannan sun kwato kayayyakin da aka sace waɗanda darajarsu ta kai naira miliyan 217,664,618.00.
Ya ce sojoji sun kuma kwato lita 201,700 na ɗanyen mai da lita 88,177 na gas (AGO) a cikin wannan watan.
Hedikwatar Tsaro ta yaba wa sojojin saboda jarumtarsu kuma ta yi kira da su ci gaba da zage damtse kan turmushe ayyukan ‘yan ta’adda.














