ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Kamata Amurka Ta Daina Sa Hannu Cikin Harkokin Najeriya

by CGTN Hausa and Sulaiman
9 months ago
Amurka

Bisa labarin da jaridar ‘The Punch’ ta Najeriya ta bayar, an ce, a kwanan nan kwamitocin majalisar dokokin Amurka sun gudanar da taro, don tantance lamuran garkuwa da mutane da ke faruwa a Najeriya, da kuma batun zargin da aka yi cewa wai ana cin zarafin Kiristoci a kasar. Kafin hakan, shugaban Amurka Donald Trump ya furta a shafinsa na sada zumunta cewa, Najeriya ta zama “wuri mai barazana ga rayuwar mabiyan addinin Kirista”, ya kuma sake sanya Najeriya a cikin jerin kasashe da ake sa musu kulawar musamman bisa dokar ‘yancin addini ta kasa da kasa, kana ya umurci ma’aikatar tsaro ta Amurka, da ta shirya wajen daukar matakin soji a Najeriya idan hakan ya zama wajaba.

To ko me ya sa Amurka ta sa hannu cikin harkokin gidan Najeriya ba zato ba tsammani? Kuma ko mene ne ainihin burinta?

Lallai, Amurka tana zargin Nijeriya da “cin zarafin Kiristoci a Najeriya”, amma gaskiyar lamarin shi ne, mafi yawan rikice-rikice da ke faruwa a Najeriya suna da alaka da kwaton albarkatu da rikice-rikicen kabilu, yayin da kungiyar masu tsattsauran ra’ayi ta “Boko Haram”, ke kai hare-hare ba tare da bambanta wani addini ba. Ko musulmai ma suna cikin wadanda abin ya fi shafa. Don hakan zargin na “kisan kiyashi na addini” ba shi da tushe balle makama.

ADVERTISEMENT

A bangaren siyasar cikin gidan Amurka, shugaba Trump yana amfani da “kare mabiyan addinin Kirista” don neman gamsar da masu jefa masa kuri’a mabiyan addinin kirista ‘yan bushara, don samun goyon bayansu, tare da dora laifi kan saura game da matsalolin tattalin arziki da rashin aikin yi a cikin Amurka.

A fannin tattalin arziki kuma, Najeriya a matsayinta na kasar da ta fi yawan samar da mai a Afirka, Amurka ta matsawa Najeriya lamba ne da nufin mallakar makamashinta da sauran muhimman albarkatu, tare da raunana tasirin wasu kasashe a fannin hadin gwiwar makamashi tsakaninsu da Najeriya.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

A sa’i daya kuma, Najeriya muhimmiyar kasa ce a yankin yammacin Afirka. Amurka na neman shiga fagen tsaron Najeriya ne ta hanyar fakewa da batun “hadin gwiwar tsaro”, don dakile yunkurin adawa da kasashen yamma a yammacin Afirka, tare da tilasta wa Najeriya nuna goyon bayanta.

Sai kuma ta fannin dangantakar Najeriya da Amurka, game da harajin da Amurka ta kakabawa sassa daban daban, shugaban Najeriyar Bola Tinubu ya taba cewa: “Idan kudaden shigarmu da ba na bangarorin mai ba suna karuwa, ba za mu ji tsoron duk wani abu da Trump ke yi ba.” Kazalika, a babban taron MDD na karo na 80, mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya zargin matakan da Isra’ila ta dauka a Gaza, da kuma asarar rayukan Palasdinawa da hakan ya haifar. Hakan ne ma ya sanya kafofin yada labarai na Amurka, suka karawa labaran tashe-tashen hankula na cikin gidan Najeriya gishiri, don mai da martani ga Najeriya kan wadannan batutuwa.

A duniyar yau, yawancin kasashe suna mayar da hankali kan zaman lafiya da ci gaba, suna kara hadin gwiwa don cin moriya tare. Irin wannan dabaru da Amurka ke dauka na yin barazana, da matsin lamba, da sanya takunkumi bisa karfinta sam ba su dace ba. Dole ne ‘yan Najeriya su jagoranci kansu, su magance matsalolin Najeriya da karfin kansu. Kamata ya yi Amurka ta daina sa hannu cikin harkokin cikin gidan Najeriya. (Mai rubutu: MINA)

Amurka
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Amurka
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Xi Jinping Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Faransa 

Xi Jinping Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Faransa 

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.