Sojojin Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda 16 da suka yi yunƙurin kai hari kan sansanin Sojoji na 25 a Damboa, jihar Borno, a ranar Juma’a.
Bisa rahoton LEADERSHIP, ‘yan ta’addan sun ƙara yawan hare-haren da suke kaiwa kan sansanonin Sojoji a jihar, inda wasu jaruman Sojoji suka mutu a Marte da Rann a cikin ‘yan kwanakin nan.
- Na Kwana A Marte Ne Don Ƙarfafa Gwiwar Jama’a Bayan Harin Boko Haram – Zulum
- Wasu ‘Yan Siyasa Da Jami’an Tsaro Na Taimaka Wa Boko Haram – Zulum
Duk da haka, Sojojin sun samu nasarar daƙile wannan hari ta hanyar amfani da haɗin gwuiwar rundunar sama da ta ƙasa.
Hukumar Sojojin Nijeriya ta tabbatar da cewa da ƙarfe 1 na dare ranar 23 ga Mayu, 2025, Sojojin Operation Haɗin Kai sun hango gungun ‘yan ta’addan ISWAP/Boko Haram a Damboa kuma suka fara kai musu hari.
“An tura jiragen sama don taimakawa Sojojin ƙasa, kuma bayan kusan sa’o’i biyu na faɗa, ‘yan ta’addan sun ja da baya, bayan sun sha kashi. Sojojin sun kashe ‘yan ta’adda 16 kuma suna ci gaba da bin su,” in ji wata sanarwa daga Sojojin.
Mataimakin Daraktan Ayyuka na Operation Haɗin Kai, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya tabbatar da kashe ‘yan ta’addan, yana mai cewa Sojojin na ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’addan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp