Dakarun runduna ta ɗaya ta Sojojin Nijeriya sun kashe wasu mahara 6 tare da kama wasu da ake zargin suna haɗa baki wajen aika-aika a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
A yayin farmakin, ƴan ta’addan sun bar shanun da suka sato a ƙauyen Sabon Sara, inda daga bisani Sojoji suka yi artabu da su a dandalin kasuwar Galadimawa, wanda ya yi sanadin kashe mahara shida.
- Yansanda Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kwato Kudin Fansa A Kaduna
- Rikicin Masarautar Kano: Lauyoyi Da Alƙalai Sun Tozarta Ɓangaren Shari’a – Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi
A cewar Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Sojojin sun ƙwato shanun da aka yi yasar tare da miƙa su ga mutanen yankin kafin su ci gaba da bin sahun ɓata garin.
Sojojin sun kuma kama wasu mutane uku da ake kyautata zaton suna haɗin gwuiwar aiki tare da maharan, sannan Sojojin sun ƙwato babura biyu da wayoyin hannu hudu.
Gwamna Uba Sani ya yabawa Sojojin sannan ya buƙaci jami’an tsaro da su ci gaba da gudanar da bincike domin tarwatsa wasu kungiyoyin masu aikata laifuka.