Sojojin Operation Haɗin Kai (OPHK) na Rundunar Haɗin Gwuiwa ta Arewa maso Gabas sun kashe ƴan Boko Haram tara, tare da ƙwato kuɗin fansa na Naira miliyan biyar (₦5m) a wani sumame da suka kai a Magumeri da Gajiram da ke ƙaramar hukumar Nganzai ta jihar Borno.
Wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na OPHK, Laftanar Sani Uba, ya fitar a ranar Asabar ta bayyana cewa dakarun sun kai farmaki ne bayan samun sahihan bayanan leƙen asiri kan motsin ƴan ta’addan a yankin Goni Dunari, Magumeri, a ranar 10 ga Oktoba, 2025.
- ‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno
- Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 14 A Borno Da Adamawa, Sun Ƙwato Makamai
A cewar Uba, ƴan ta’addan suna tafiya ne da motoci biyu tare da mayaƙa 24 a ƙafa, suna ƙona gidaje da tsoratar da mazauna yankin, lamarin da ya sa Sojojin suka yi gaggawar kai musu farmaki. Bayan fafatawa mai tsanani na tsawon awanni huɗu, Sojojin sun kashe ƴan ta’adda biyar yayin da sauran suka gudu da raunuka.
Kayan da aka ƙwato sun haɗa da bindigar AK-47 guda ɗaya, da mujallu guda biyar, da sinƙin harsasai 31, da wayar salula da kuma wuka. Babu asarar rai ko kayan aiki daga ɓangaren dakarun Nijeriya.
A wani sumame makamancin haka da aka gudanar a hanyar Gajiram–Bolori–Mile 40–Gajiganna, Sojojin da ke haye kan babura sun kashe ƴan Boko Haram huɗu tare da ceto mutane biyu da aka sace. An kuma ƙwato kuɗin fansa har Naira miliyan 4.35, da motar Hilux mai lamba GUB 327 XA, da wayoyi biyu da galan ɗin mai.
Uba ya ce dakarun sun ci gaba da bincike da fatattakar ƴan ta’addan don hana su sake samun damar motsi a yankin Arewa maso Gabas.