Dakarun sojojin Nijeriya sun kashe wani dan bindiga a wani harin kwanton bauna da suka kai mashigar kauyen Bura da ke karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi.
Sojojin sun kuma kwato wata mota da aka sace tare da cafke wasu mutane uku da ake zargin barayin mota ne.
- “Hanyar Siliki Ta Dijital” Na Ingiza Zamanantar Da Duniya
- Gwamnan Neja Ya Taya Ndace Murnar Nadinsa Shugaban VON
Sanarwar da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya ce sojojin da ke aiki da bayanan sirri sun yin artabu da ‘yan bindigar, inda suka kashe daya daga cikinsu, yayin da wasu suka gudu da harbin bindiga.
Sojojin sun kwato bindigu kirar AK-47 guda 14 harsashi da dama, wayar hannu daga hannun ‘yan fashin.
A wani labarin kuma, ya ce dakarun sun kama wasu gungun barayin motoci uku a kan hanyar Bauchi zuwa Jos.
Ya ce sojoji bayan samun rahoton sun yi gaggawar tare wani shingen binciken ababen hawa a kan babbar hanyar inda suka yi nasarar cafke masu laifin.
Ya kara da cewa, ‘yan ta’addar sun yi yunkurin tserewa bayan da suka ga sojojin.
Sojojin sun damke barayin kuma tuni suka mika su da motar da suka sace ga rundunar ‘yan sandan Nijeriya domin ci gaba da bincike.