Dakarun Nijeriya sun kashe wani babban kwamandan ƙungiyar Boko Haram/ISWAP mai suna Ibn Khalid a wani artabu da ya gudana a ƙaramar hukumar Gwoza, jihar Borno. Wannan kwamandan na daga cikin masu shirya hare-hare da yaɗa bidiyon labaran ƙungiyar ga mabiyanta.
Wannan nasara ta biyo bayan wani samame da Sojojin Operation Haɗin Kai suka kai a yankin Bitta, inda suka daƙile yunkurin ƴan ta’addan na kutsawa cikin garin. An yi artabu mai zafi wanda ya kai ga hallaka ƴan ta’adda da dama, ciki har da kwamandan da mai ɗaukar bidiyo.
- Sin Ta Yi Mu’amala Da Kasashen Dake Kan Karshen Kogin Yarlung Zangbo Dangane Da Batun Gina Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Karfin Ruwa A Kogin
- Sojoji Sun Kashe Kwamandan Ƙungiyar Haram/ISWAP Da Wasu 5 A Chadi
Kyaftin Reuben Kovangiya, mai magana da yawun rundunar, ya bayyana cewa dakarun sun kwato makamai da dama ciki har da bindigu, da harsasai, da babura da kyamarar ɗaukar bidiyon da suke amfani da ita wajen yaɗa hare-harensu. Ya ce an kuma daƙile wani hari da suka shirya kaiwa Monguno.
Baya ga haka, Sojojin sun kai wasu hare-hare a dajin Sambisa har zuwa Madagali da Kaga, inda suka kashe ƴan ta’adda 17 tare da lalata sansanoninsu.
Rundunar Operation Hadin Kai ta jinjina wa jarumtakar dakarunta, tana mai cewa za su ci gaba da fatattakar ƴan ta’adda daga kowanne sashi har sai an gama da su gaba ɗaya. Ana kuma kira ga al’umma da su riƙa ba da bayanai domin taimakawa Sojojin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp