Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Whirl Stroke sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin ’yan bindiga ne a wani artabu da suka yi a kan hanyar Adankolo zuwa Apata a Jihar Kogi.
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce an gudanar da aikin ne ranar Asabar bayan samun bayanan sirri kan motsin wasu da ake zargin masu aikata laifuka ne a yankunan ƙananan hukumomin Kabba-Bunu da Lokoja.
Sojojin sun yi wa waɗanda ake zargin kwanton bauna a wata hanya, lamarin da ya tilasta musu tserewa.
Bayan gudanar da bincike, sojojin sun gano gawarwakin mutane biyu da ake zargin ’yan bindiga ne a dajin Adankolo.
Haka kuma, sun ƙwato bindiga ƙirar gida guda ɗaya, harsashi guda ɗaya da kuma kwanson harsashin bindiga mai nau’in 7.62mm.
Kwamandan rundunar, Manjo Janar Moses Gara, ya yaba wa sojojin bisa nasarar da suka samu tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai domin taimaka musu wajen yaƙi da aikata laifuka.













