Dakarun Sojojin Nijeriya sun hallaka wasu mutane biyu da ake zargin ’yan bindiga ne, bayan sun yi musu kwanton ɓauna a kan hanyar Adankolo–Apata da ke Jihar Kogi, yayin wani samame da suka kai bisa sahihan bayanan sirri.
Dakarun Sashe na 3 na Rundunar Haɗin Gwiwa ta ‘Operation Whirl Stroke’ ne suka gudanar da aikin a ranar Asabar, bayan samun bayanan sirri kan zirga-zirgar wasu da ake zargin masu aikata laifuka ne a yankunan Ƙananan Hukumomin Kabba-Bunu da Lokoja.
A cewar wani saƙo da Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na hedikwatar rundunar ya wallafa a shafin X na Rundunar Sojin Nijeriya, dakarun sun yi kwanton ɓauna a wata hanyar da ake zargin masu aikata laifukan na amfani da ita wajen jigilar kayayyaki.
Sanarwar ta bayyana cewa dakarun sun yi arangama da ‘yan ta’addan, lamarin da ya tilasta musu tserewa.
Sai dai, yayin wani bincike da suka gudanar daga baya a safiyar ranar, sojojin sun gano gawarwakin mutane biyu da ake zargin ’yan bindiga ne a yankin Dajin Adankolo.














