Hadakar jami’an tsaro sojin kasa da na ruwa sun hallaka ‘yan bindiga bakwai a yayin wani samamen kakkebe ‘yan ta’adda a yankin Kasso da ke karamar hukumar Chikum a Jihar Kaduna.
A wata sanarwar manema labarai da Kwamishinan Kula da Harkokin Tsaron Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar a ranar Juma’a, ya ce, bayanan da gwamnatin Jihar Kaduna ta samu na sakamakon aikin, ya yi nuni da cewa sojojin sun cimma ‘yan bindigae ne a wajen kauyen Ungwani Rimi da ke Kasso a kusa da wani ruwa.
- NEF Ga Buhari: Kar Ka Sake A Karkashin Mulkinka Ka Bari IPOB Ta Hana ‘Yan NIjeriya Kada Kuri’a
- Arewa An Sha Mu Mun Warke, Bai Kamata Mu Koma Gidan Jiya Ba –Matasan Arewa A Kudu
Sanarwar ta ce, haduwar tasu ke da wuya sojojin sun sha karfin ‘yan bindigar a lokacin da suka gwabza fada a tsakaninsu.
Aruwan, ya kara da cewa sojojin sun kwato babura guda biyar, alburusai guda 153, da wasu alburusai guda bakwai tare da wayoyin hannu guda uku a lokacin arangamar.
“’Yan bindiga bakwai ne aka tabbatar da kashesu a yayin harin, tare da tunanin wasu ma za su iya bin sawunsu da wadanda suka jikkata a kusa da wani kogi.
“Lokacin da ya samu rahoton, gwamna Nasiru El-Rufai ya jinjina tare da yaba wa kokarin dakarun sojojin tare da fatan za su kara ninka kokarinsu domin dakile aniyar ‘yan bindiga a jihar
“Sannan, gwamnan ya kuma jinjina wa jagorancin Manjo-Janar TA Lagbaja, GOC na runduna ta daya da Cdre ME Ejumabone, kwamandan kwalejin horas da sojojin ruwa NNSAT, bisa nasarorin da suka samu,” in ji Aruwan.