Sojoji a Jihar Sakkwato, sun kashe wasu ’yan bindiga a ranar Litinin tare da ceto ’yan kasuwa da aka sace a kan hanyar Tarah zuwa Karawa da ke Sabon Birni.
’Yan kasuwar sun fito daga ƙauyen Tarah kuma suna kan hanyarsu na zuwa kasuwar mako-mako da ke Sabon Birni lokacin da aka kai musu hari da misalin ƙarfe 8 na safe.
- Za A Fara Gasar Wasanni Ta Nakasassu Da Masu Bukata Ta Musamman Ta Sin
- Sin Ta Kira Taron Binciken Ayyukan Tattalin Arziki Na Shekarar 2026
Sojojin da ke Kurawa sun yi gaggawar zuwa wajen bayan jin harbe-harbe, inda suka yi artabu da ’yan bindigar na kusan awa guda.
Daga baya ’yan bindigar sun tsere.
Sojojin sun gano gawarwakin mutum tara a wajen, sannan sun gano wasu mutane huɗu a cikin daji da kusa da rafin.
Sun kuma ƙwato makamai da babura.
An ceto dukkanin ’yan kasuwar ba tare da sun ji rauni ba, sai dai mutane biyu da suka jikkata kuma suna jinya a asibiti.
Babu wani soja da ya rasu ko ya ji rauni.
Al’ummar Kurawa da maƙwabtansu sun yi murna da nasarar wannan samame.
Ɗan majalisar jihar, Aminu Boza, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa bincike na ci gaba da wakana a yankin.
Harin ya faru ne kwana guda bayan ’yan bindiga sun kashe mutane bakwai tare da sace mata da dama a ƙauyukan Gatawa da Shalla a yankin.














